1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda sun far wa masu bore a Nijar

October 29, 2017

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa, an samu arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga a Yamai babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/2mhnE
Niger Anti Charlie Hebdo Protest Polizeieinsatz 18.01.2015
Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

Kungiyoyin fararan hula ne dai suka kira zanga-zanga nuna adawa da sabuwar dokar samar da kudi tafi da gwamnati, wadda za tafara aiki daga badi, wadda suka ce ta saba wa halin rayuwar da al'uma ke ciki. 'Yan sandan sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa dubban masu zanga-zangar, inda daga nasu bangare masu zanga-zangar suka mayar ta martani da duwatsu.

Dubban mutane ne dai suka hallara yayin wannan zanga-zanga a wani fili da ake kira ''Place Tumo'' da ke tsakiyar birnin na Yamai, inda aka tsara gabatar da jawaban yin watsi da sabuwar dokar.