1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Yan sandan Jamus sun cafke 'yan IS kan azabtar da Yazidi

April 10, 2024

'Yan sandan Jamus sun cafke wasu ma'aurata a kudancin jihar Bavaria da ake zargin 'yan kungiyar IS, sakamakon cin zarafi da hana wasu 'yan mata na Yazidi biyu da sukayi a tsakanin 2015 zuwa 2017.

https://p.dw.com/p/4edUN
Wasu 'yan matan Yazidi dauke da hotunan mazajensu da aka kashe a Iraqi
Wasu 'yan matan Yazidi dauke da hotunan mazajensu da aka kashe a IraqiHoto: Creative Touch Imaging/NurPhoto/picture alliance

'Yan sandan sun dai cafke mutanen biyu ne domin jin ba'asi kan azabtar da 'yan matan, da ke da tsatso da Yazidi da ke da matukar tasiri a kasashen Iraqi da Siriya.

Karin bayani: Jamus na neman kwato wa 'yan Yazidi hakki

Babban mai gabatar da karar jihar Bavaria ya ce mutanen biyu da ke kasancewa ma'aurata sun azabtar da yaran ne ta hanyar cin zarafinsu da wulakantasu harma da hana su gudanar da addininsu. Ya kara da cewa bayan azabtar da yaran ta hanyar killace su a Iraqi, daga bisani sun mika su ga kungiyar IS kafin su tsallako zuwa kasar Jamus.

Karin bayani: Tsananin damuwa bai kare ba ga yara 'yan kabilar Yazidi a Iraki

Kazalika, cafke su na nasaba da kudurin majalisar dokokin Jamus na bayyana cin zarafin 'yan Yazidin a matsayin kisan kare dangi. Yazidi sun fito daga kabilar Kurdawa marasa rinjaye da galibinsu ke arewacin Iraqi.