1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan siyasan na neman kafa gwamnati

April 22, 2013

Shugaban Italiya Giogior Napolitano ya nemi 'yan siyasa su kawo karshen zaman doya da manja kan kafa sabuwar gwamnati ta gaba.

https://p.dw.com/p/18Kxu
Hoto: Reuters

Shugaban kasar Italiya Giogior Napolitano, ya bukaci jam'iyyun siyasan kasar su cimma matsaya kafa sabuwar gwamnati, ba tare da bata lokaci ba, sannan ya zarge su da toshe kunne kan bukatun mutane.

Shugaban ya bayyana haka yayin rantsawar wa'adi na biyu na mulkin shekaru bakwai a gaban majalisar dokokin kasar, bayan zabensa karo na biyu a karshen mako. Watanni biyu bayan zaben kasa baki daya 'yan siyasa sun kasa cimma matsayar kafa gwamnati, saboda babu jam'iyyar da ta samu rinjayen da ta ke bukata, domin nada firaminista.

Napolitano dan shekaru 87 da haihuwa ya ce, muddun 'yan siyasa ba su cimma matsaya ta kafa gwamnati, lallai zai dauki mataki na gaba, haka na nufin ko ya yi murabus ko kuma ya kira sabon zabe. Ya zama mutun na farko da ya sake samun wa'adi na biyu na mulkin shekaru bakwai, yayin zaman hadin gwiwa na majalisu dokokin kasar cikin karshen mako.

Muddun aka cimma matsayar da ake bukata za a nada firamistan na gaba, kuma wasu kafofin yada labaran kasar ta Italiya sun ce, akwai yuwuwar Giuliano Amato dan shekaru 75 da haihuwa tsohon firaminista, ya sake samun mukamun, domin kafa gwamnati da za ta kunshi kwararru da 'yan siyasa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu