1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun halaka mutane 11 a jihar Borno

November 6, 2023

Wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyoyin ta'adda ne sun halaka akalla mutane 11 a wasu gonakin shinkafa a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/4YTkZ
'Yan ta'adda sun halaka mutane 11 a jihar Borno
'Yan ta'adda sun halaka mutane 11 a jihar Borno Hoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Wata majiya daga yankin ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa lamarin ya auku ne a daren Lahadi wayewar Litinin, sannan kuma baya ga asarar rayuka mutane da dama sun yi batan dabo yayin da wadansu mutanen hudu suka jikkata.

Karin bayani: Jama'a na yin tir da hare-hare a Borno da Yobe

Majiyoyi daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar sun ce an gudanar da jana'izar mamatan 11 da maraican Litinin (06.11.2023) a babban masallaci na Zabarmari a karkashin mahukuntan yankin.

Karin bayani: Boko Haram ta kai sabon hari a Borno

Hare-haren kungiyoyin Boko Haran da ISWAP sun raunana tafiyar harkokin noma da kiwo da kuma kamun kifi a wannan yankin na Arewa maso gabashin Najeriya, inda 'yan ta'addar ke zargin al'umma da bai wa sojoji bayanai a game maboyarsu.