1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan takara 20 sun janye daga yaƙin neman zaɓe a RDC

July 4, 2006
https://p.dw.com/p/Burd

A Jamhuriya Demokradiyar Kongo, a na ci gaba da yakinnemanzabe, to saidai yan takara 20 daga jimmilar yan takara 33 masu neman kujera shugabacin kasa, sun hido sanarwar hadin gwiwa,a yau talata inda su ka buƙaci a dakatar da yaƙin neman zaɓen da ma zaɓen kansa, har lokacin da aka cimma daidaito tsakanin ɓangarorin siyasa daban-daban na ƙasa.

Yan takara 20, sun ɗauki wannan mataki a sakamakon abinda su ka kira maguɗi, da ke tattare da yaƙin neman zaɓen.

Cemma dai Jam´iyar adawa ta Etienne Cissekedi, tunni, ta ƙauracewa zaɓe.

A nasa ɓangaren, shugaban ƙasa Joseph kabila, wanda shima ɗan takara ne, a ƙarƙashin tutar Indipenda, ya gana yau, da ministan tsaro na ƙasar Jamus Franz Josef Jung.

Kabila ya bayana gamsuwa, a game da matakin da ƙungiyar gamaya turai, ta ɗauka na aika dakaru, domin sa iddo a zaɓen da za ayi.

A nasa gefen ministan tsaron Jamus ya yaba yada al´umma ta karɓi dakarun na EU cikin raha da farin ciki.