1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Seleka sun bayar da kai...

January 11, 2013

Yan tawayen jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun cimma yarjejniyar zaman lafiya da gwamnati inda suka amince Bozize ya ci gaba da mulki tare da kafa gwamnatin hadin kan kasa.

https://p.dw.com/p/17IiP
Hoto: dapd

Kungiyar 'yan tawayen Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta amince shugaba François Bozize ya kammala wa'adinsa kafin ya sauka daga kujerar mulki. Wannan kudirin dai na kunshe ne cikin yarjejeniyar zaman lafiya da bangarorin biyu suka cimma a wannan juma'ar a birnin Libreville na Gabon. Daga cikin muhimman batutuwa da yarjeejniyar ta kunsa har da tsagaita bude wuta tsakanin sojojin gwamnati da kuma 'yan tawayen Seleka, da kuma kafa gwamnatin hadin kan kansa, tare da gudanar da zaben 'yan majalisa nan da watannin 12 masu zuwa.

Bangarorin biyu sun amince sojojin kasashen waje su fice daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, amma ban da wadanda suke aikin kiyaye zaman lafiya karkashin jagorancin kungiyar tsaro ta CEEAC. Tun dai a ranar 10 ga watan disemba na shekarar da ta gabata ne kungiyoyin tawaye uku da suka hade karfinsu guri guda suka karbe ikon birane da dama da nufin hambarar da gwamnatin François Bozize. Suna zarginsa da rashin cika alkawarin da ya yi a baya na inganta rayuwar tsaffin 'yan tawayen ta hanyar samar musu da guraben aiki.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal