1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Tunusiya na jajirce wa ta'addanci

Suleiman BabayoNovember 26, 2015

'Yan Tunisiya na kokarin gudanar da hidimominsu na yau da kullau a kasar bayan hare-haren da tsagerun kungiyar IS suka dauki nauyin kaiwa a Tunis babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/1HCyC
Tunesien Tunis Anschlag auf Militärfahrzeug
Hoto: Sarah Mersch

'Yan Tunusiya na jajirce wa ta'addanci

Kwana guda bayan harin da aka samu a birnin Tunis fadar gwamnatin kasar Tunisiya, matasa sama da 100 ne suka sayi tikitin shiga kallon bikin nuna fina-finai. Sofia 'yar makaranta da ke da shekaru 19 da haihuwa ta yi korafin cewar "Kullum abin da muke gani ke nan sai hare-haren ta'addanci. " Saboda haka ne take ganin cewar ya dace jami'an tsaro su shawon kan irin hare-haren ta'addanci da ake samu.

Ita kuwa Faten Abdelkefi wacce ta saba halartar bikin nuna fina-finai ta ce nuna turjiya ya na da muhimmanci. Ta ce " A ko'ina mutum zai iya mutuwa, idan a gidan kallo ne ma hakan zai iya kasance."

Sai dai Abdelkefi na jin tsoron irin abin da ke faruwa, amma ba zai sata zama a gida ba. Ta ce" Idan kowani yammaci mutum zai zauna a gida saboda tsoro, haka zai bai wa 'yan ta'adda nasara. Amma kar mu yarda su samu nasara."

Tunesien Anschlag in Tunis auf Bus der Präsidentengarde
Hoto: Reuters/Z. Souissi

Akwai daruruwan baki wadanda suka saba zuwa wajen bikin na nuna fina-finai a babban birnin kasar ta Tunisiya. Kuma kwana daya bayan harin da aka samu a birnin na Tunis ministar kula da al'adu ta kasar Latifa Lakhdar ta bayyana matakan tsaro da aka dauka domin kare wadanda suke halartar wannan biki sannan ta kara da cewa: Ta ce "Za mu ci gaba da rayuwa kamar yadda muka saba, haka muke son rayawarmu"

Gwamnati ta tsaurara matakan tsaro a Tunisiya

Gidajen kallo da hotel-hotel da baki masu zuwa bikin nuna finai-finai suke zama da ke cikin birnin Tunis ya kasance 'yan mitoci daga wurin da aka samu wata fashewa. Sannan daga bisani da rana bam ya tarwatsa wata motar safa dauke da jami'an tsaron shugaban kasa lokacin da suke kan hanyar zuwa aiki. Wurin da lamarin ya faru ya na kusa da ma'aikatun cikin gida da na kula da yawon bude ido.

Mutane 12 daga cikin wadanda suka hallaka jami'an tsaro ne, saura kuma ana zaton maharan ne. Babu bayani kan yadda maharin ya kutsa kai cikin wannan motar safa. Sai dai binciken farko ya nuna bam da aka tayar ya kai nauyin kilogram 10.

Tunesien Tunis Anschlag auf Militärfahrzeug
Shugaba Essebsi ya ce zai ci gaba da yaki da ta'addanciHoto: Getty Images/C. Somodevilla

Shugaba Beji Caid Essebsi na kasar ta Tunisiya ya ce kasar ba za ta mika wuya ga ayyukan ta'addanci ba, inda ya ce "burin 'yan ta'adda shi ne saka tsoro da fargaba, amma a karshe su ne za su ji tsoron."

Tuni mahukuntan Tunisiya suka rufe iyakar kasar da Libiya wadda take cikin tashin hankali, wacce kuma ake gani ana horos da mayaka masu kai irin wadannan hare-hare a cikinta.