'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Manuel Neuer

Mai tsaron gidan na Jamus yana cikin koshin lafiya yayin da ake shirin tafiya gasar. Duk da ya tafi dogon hutu sakamakon rauni, jagoran 'yan wasan na zama mai tsaron gida shi ne na farko a jerin masu tafiya wasan na Rasha.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Marc-André ter Stegen

Shi ke zama mai tsaron gida na farko a kungiyar Barcelona wanda kuma ba ya daga cikin masu wasa ga kungiyar kwallon kafa ta kasa a baya. Stegen ke zama lamba na biyu a gasar ta neman cin kofin kwallon kafa na duniya.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Kevin Trapp

Mai horas da 'yan wasan Löw ya dauko mai tsaron gidan wanda ya yi wasa da Paris St. Germain kafin zuwa South Tyrol. Sai dai tun a Paris St. Germain ya hau benci saboda ba shi ne zabin farko ba lamarin da ya janyo rashin buga muhimmin wasa.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Jerome Boateng

Tun bayan samun rauni a watan Maris akwai zaman zullumi kan tafiyar dan wasan mai tsaron baya zuwa gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a Rasha. Boateng kullum na cike da fata kuma da wannan fata zai tafi gasar ta Rasha.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Mats Hummels

Dan wasa na Bayern Munich kan hada karfi da Boateng saboda karfafa bayan Jamus. Kuma lokacin bude gasar Hummels na cikin masu tasiri ga mai horas da 'yan wasan na Jamus Joachim Löw.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Antonio Rüdiger

Yana cikin 'yan wasa biyu masu tsaron baya da ke zaman jira. Dan wasan na Chelsea ya samu kwarin gwiwa daga mai horas da 'yan wasan Joachim Löw.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Niklas Süle

A matsayin mai yin sauyi yana cikin matasa 'yan wasan baya na Bayern. Sai dai zai yi wuya ya fito sosai lokacin gasar ta neman cin kofin kwallon kafa na duniya.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Joshua Kimmich

Mai tsaron bayan na Bayern yana bangaren tsaron baya ta dama. Ya kan yi kuma wasan tsakiya, wani lokacin mai horas da 'yan wasan Löw kan jefa shi gaba saboda yana da hadari.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Jonas Hector

Bahagon dan wasan baya ya samu matsalar rauni lokacin wasannin lig da yake wasa a kungiyar FC Kolon. A bangaren hagu ya kasance shi ke zama zabi na farko a kungiyar ta kasa.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Marvin Plattenhardt

Babu 'yan wasan baya da yawa haka yake tsakanin 'yan wasan Jamus. Ga mai horas da 'yan wasan Löw, shi matashin dan shekaru 26 ya zama zabi na biyu ga Hector.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Matthias Ginter

Gwarzon dan wasan duniya ko bai yi wasa ba a gasar shekara ta 2014, mai horas da 'yan wasan Löw yana jin dadin Ginter kan iya shiga kowane bangare. Wasan da ya yi a kungiyar Borussia Mönchengladbach babu wani karsashi.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Sami Khedira

Dan wasan na baya na Jeventus ya kasance mai wasan tsakiya a kungiyar kwallon kafa ta kasa.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Toni Kroos

Kamar Khedira shi dai Toni Kroos yana wasa a kungiyar da ta shahara a Turai ta Real Madrid tare da nuna bajinta.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Sebastian Rudy

Wannan hazikin dan wasa na Bayern yana cikin masu tafiya Rasha. Rudy ba koyaushe yana cikin na farko masu buga wasa a Bayern ba. Yana wasan baya da tsakiya.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Ilkay Gündogan

Ya gaza zuwa gasar cin kofin duniya na shekara ta 2014 sakamakon ciwon baya, da kofin nahiyar Turai shekaru biyu daga bisani saboda rashin samun sauki. Wannan lokaci yana shirye da tafiya gasar.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Mesut Özil

A kwallo ya kasance mai basira lokacin wasa, amma ba kasafai yake nuna kansa ba lokacin wasa mai tasiri. Sai dai mai horas da 'yan wasa Löw ya ki sadaukar da wannan dan wasa mai tasiri na Arsenal.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Thomas Müller

"Müller yana wasa koyaushe" a cewar mai horas da 'yan wasan Bayern Munich Van Gaal. Haka lamarin yake ga dan wasan mafi jefa kwallo a raga cikin kungiyar kwallon kafa ta kasa tun daga shekara ta 2010.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Marco Reus

A karshe dan wasan na Dortmund zai tafi gasar neman cin kofin kwallon kafa ta duniya. A shekara ta 2014 galibi dan wasan na gaba yana kan benci.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Julian Draxler

A Paris St. Germain akwai yuwuwar tsohon dan wasan na Schalke da Wolfsburg ya samu damar buga wasanni da dama. Ya kasance dan wasan gaba mai kai hari cikin gaggawa ga kungiyar kwallon kafa ta kasa.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Leon Goretzka

Bayan kammala wasan lig da nuna gwazo a kungiyar Schalke yana da kwarin gwiwa a kungiyar kwallon kafa ta kasa. Zai iya fitowa sosai lokacin gasar ta Rasha.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Timo Werner

Amfani da karfi da tafiya cikin hanzari ya kasance kan gaba wajen jefa kwallo a raga. Dan wasan na Leipzig yana cikin 'yan wasan gaba da mai horas da 'yan wasa Löw ke gadara da su.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Mario Gomez

Dan wasan gaba na Stuttgart yana cikin wadanda mai horas da 'yan wasa Löw ya dauko domin ya samu abin da yake bukata. Gomez ya buga gasar cin kofin Turai a Faransa, har zuwa lokacin da ya samu rauni a wasan kusa da na karshe.

'Yan wasan Jamus na kofin duniya na 2018

Julian Brandt

Mai basira na kungiyar Bayer Leverkusen ya kasance mai dauriya. Zuwa cin kofin kwallon kafa na duniya ya zama sakamakon da ya samu.

Mai horas da 'yan wasa na kasa Joachim Löw yana da burin kare kofin na duniya da 'yan wasan lokacin gasar ta Rasha. Ga 'yan wasan 23 da Löw ya zakulo zuwa gasar ta 2018.