1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zafi ya yi kamari a Kano

April 9, 2019

Zafin rana mai tsanani da ake fama da shi a jihar Kano na cigaba da hana jama'a walwala saboda rashin samun kariyar da ya kamata su yi wa kansu.

https://p.dw.com/p/3GVc6
Australien - Pferde
Hoto: Imago/Photocase/Daviles

 

A wannan lokaci da zafin ranar kan zarta degree 40 a ma'aunin zafi, babu abunda jama'a suka fi yi face yawaita shan ruwan sanyi da wanka da ruwan sanyin, a daidai lokacin da suke cigaba da gudanar da harkokinsu a takure.

Direbobi da ke tafiya mai dogon a yankin arewacin Najeriyar, sun koka da yanayin na zafi, sai dai sun ce idan suka tsaya ne lamarin yafi yawa, domin a yayin da suke tafiya iska na dan fifitasu.

Wasu 'yan kasuwa da ke tafiyar da harkokinsu na kasuwanci a kan ranar kuwa, sun koka da hali mawuyaci da suke ciki, inda wasu kan koma gida su dan watsa ruwan sanyi, kafin su sake komawa bakin harkokinsu na kasuwanci. A yayin da wasu da ba zasu iya komawa gida ba kan bi inuwa inuwa domin samun saukin lamarin.

Su ma dabbobi a ba a barsu a baya ba na jin radadin yanayin na zafi, saboda karancin abinci.