1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yanayin zamantakewa a Maiduguri sakamakon rashin tsaro

Ahmed SalisuSeptember 23, 2014

Al'ummomin da ke kewaye da Maiduguri na zama cikin fargaba da rashin tsaro, kuma ba su amince da matakan gwamnati ba, a cewar Bishop Oliver Dashe, jagoran darikar Katolika a Maiduguri, jihar Borno.

https://p.dw.com/p/1DJ8L
Angriff von Boko Haram im nordöstlichen Stadt Konduga nahe Maiduguri / Nigeria
Hoto: dpa

Shugaban mabiya darikar katolika na gundumar Maiduguri da wasu jihohin arewa maso gabashin Najeriya, Bishop Oliver Dashe Doeme, ya nuna rashin gamsuwarsa dangane da yadda gwamnatin Najeriya ke tinkarar yaki da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram.

Bishop Dashe ya ce jama'a na fama da matsaloli sosai domin da yawa sun rasu wasu sun rasa matsugunnensu kuma adadin yara marayu ya karu sosai sanan babu wani yunkurin da gwamnati ta yi na biyan bukatun wadannan mutane, ko da a gajeren lokaci ne ga shi kuma yanayin rayuwa na kara matse musu.

Fargaba a Maiduguri - Bishop Dashe

Bishop din ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Ahmed Salisu inda ya fara shaida masa halin da yanzu haka ake ciki a garin Maiduguri na jihar Borno.