1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara mata da ke haifuwa sun karu

October 30, 2013

Wani rahoton hukumar kula da yawan al'umma ta duniya ya koka dangane da yawaitar yara kanana da ke samun juna biyu wanda ya ce hakan na da illa ga lafiyarsu.

https://p.dw.com/p/1A9Jb
Mothers and babies wait in feeding staion. Mothers and babies waiting at World Food Programme health and nutrition station. Foto: DW/Imogen Foulkes, April 2011, Camp l'Aviation, Port au Prince, Haiti
Hoto: DW

A cikin wani rahoto da ta wallafa, hukumar kula da yawan al'umma ta duniya ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce galibin wannan matsalar an fi samunta ne a kasashe masu tasowa.

Werner Haug daya ne daga cikin daraktocin hukumar ya ce "yara mata kimanin miliyan bakwai da dubu dari uku ne ke samun juna biyu a kowacce shekara, kuma miliyan biyu daga cikin wannan adadin 'yan kasa da shekaru sha biyar ne. Yanayin girmansu da ma hankalinsu bai kai a ce sun zama iyaye ba."

Daga cikin wannan adadi da rahoton ya ce ana samu a kowacce shekara, 'yan shekaru sha hudun da aka ce sun kai miliyan biyu sun fi fuskantar matsaloli sama da saura. Wani batu da rahoton ya haska shi ne yanayin da yaran ke haifuwa duba da girmansu da yawan shekarunsu kamar dai yadda Werner Haug ya yi tsokaci.

Cambodian orphan Vannak, a 2 month old boy, HIV positive, is fed formula milk by a nanny at Chrey Chao commune orphanage on the outskirts of Phnom Penh Wednesday May 12, 2004. Despite complaints that some adopted Cambodian babies were bought or stolen - and the suspension of adoptions from Cambodia by the United States and some European nations - other Western countries have continued to allow adoptions of Cambodian youngsters. At least 91 such adoptions by British, Australian, Italian and German citizens have been approved by their governCambodia-Adoptionsments since 2001, when the United States became the first country to halt such adoptions (AP Photo/Andy Eames)
Hoto: AP

"Galibin irin wannan haihuwar da ake samu, ana yinta ne ta hanyar yi wa matan da ke dauke da juna biyu tiyata maimakon su haihu da kansu. In aka yi rashin sa'a babu kyakkyawan tsari na kiwon lafiya to a kan ci karo da matsaloli wanda kan kai ga jawo rasa ran mai jegon ko na abin da ta ke dauke da shi."

Rahoton dai ya danganta wannan matsala da ake samu da talauci da kuma rashin ilimi da ma dai sauran matsalolin da kasashe masu tasowa ke fuskanta na rashin cigaba. Har wa yau rahoton ya ce irin wannan matan na daukar cikin ne ba tare da suna da muradin yin hakan ba sai dai kawai don basu da wani zabi da ya wuce hakan.

***ACHTUNG: Nur zur Berichterstattung über die Behandlung dieser Kinder in Essen verwenden!*** Malika Bund Eljer Abaeva Im Uniklinikum Essen werden derzeit 2 Babies aus Moldawien behadelt, bei denen Retinoblastom diagnostiziert worden ist. In Moldawien gibt es für diese Krankheit kein adäquates Therapiezentrum. *** Bilder von Olga Kapustina, Deutsche Welle, 28. März 2013
Wata 'yarinyar rike da jaririntaHoto: DW/O.Kapustina

A wata zantawa da ya yi da manema labarai a birnin London dangane da wannan rahoton, shugaban hukumar ta kula da yawan al'ummar ta Majalisar Dinkin Duniya Dr. Babatunde Osotimehin cewa ya yi "Ummul aba'isin matsala ba za ta rasa nasaba da rashin sanya yara mata a makaranta da tabarbarewar fannin kiwon lafiya da ma dai rashin aikin yi."

Tuni dai masana irin su Renate Baehr da ke wata gidauniya da ke sanya idanu kan yawan al'umma a duniya ,suka fara nuna rashin gamsuwarsu, har ma suka ce barin wannan matsala na faruwa tauye hakkin yaran ne.

"Hujja ta dangane da batu na tauye hakki, ita ce yadda yara mata 'yan shekaru sha uku da haifuwa ke daukar ciki ba tare da son ransu ba. Hakan na gurgunta rayurwasu matuka."

Wannan yanayi da ake ciki ne dai ya sanya hukumar ta kula da yawan jama'a ta duniya, ke ganin dole a tashi tsaye wajen ganin an kawo karshen wannan matsala ta hanyar shimfida tsare-tsare da za su kai ga kawar da ita.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman