1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a yi musayar fursunoni a yakin Yemen

Gazali Abdou Tasawa
December 11, 2018

Gwamnatin Yemen da 'yan tawayen kasar wadanda yanzu haka ke taro a kasar Sweden domin shawo kan rikicin kasar a bisa jagorancin MDD sun sanar da cimma matsaya kan batun musayar fursunoni dubu 15 a tsakaninsu. 

https://p.dw.com/p/39tpx
Schweden Friedensgespräche für Jemen starten vor Drohkulisse
Hoto: Reuters/TT News Agency/S. Stjernkvist

Daga cikin fursinonin da matakin musayar zai shafa akwai 'yan asalin kasashen Saudiyya da Hadaddiyyar Daular Larabawa. Yarjejeniyar dai ta tanadi kwashe fursinonin ta hanyar amfani da filayen jiragen sama na birnin Seyoun na tsakiyar kasar da ke hannun gwamnati da kuma na birnin Sanaa wanda ke a hannun 'yan tawaye da ke rufe yau shekaru uku. 

Batun bude hanyoyin kai kayan agaji da kuma filin jiragen sama na birnin Sanaa da kuma tashar ruwan Hudeida na a sahun gaban batutuwan da gwamnatin Abed Rabbo Mansour Hadi mai samun goyon bayan Saudiyya, da kuma 'yan tawayen Houthis masu samun goyon bayan Iran, ke son shawo kansu a wannan taro da suka soma tun a ranar shida ga wannan wata a kauyen Rimbo na kusa da birnin Stocholm na kasar ta Sweden.