1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar Ukraine tana fuskantar barazana

Suleiman BabayoFebruary 16, 2015

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta Ukraine tana fuskantar barazana daga ɓangarorin da ke rikici da juna.

https://p.dw.com/p/1EccC
Ukraine Unruhe in Debaltseve
Hoto: Reuters/G. Garanich

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta gabashin Ukraine na fuskantar barazana kwanaki biyu da fara aiki sakamakon tahsin hankalin da ake samu kusa da wata tashar jigin ƙasa. Ƙungiyar ƙasashen Turai ta taimka aka ƙulla yarjeniyar tsakanin gwamnatin Ukraine da 'yan awaren gabashin ƙasar da ke samun daurin gindin ƙasar Rasha.

Tun farko Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nuna ƙwarin gwiwa kan ɗorewar yarjejejiyar tsagaita wuta da aka fara aiki da ita tsakanin Ukraine da 'yan awaren gabashin ƙasar, duk da damuwa kan wasu matsaloli. Mai magana da yawun shugabar Steffen Seibert ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai.

'Yan awaren sun ce za su janye makamai ne kawai idan aka fara aikin da cikakken shirin tsagaita wuta kamar yadda aka tsara a wajen taron birnin Minsk na ƙasar Belarus a makon jiya. Ƙarƙashin yarjejeniyar an buƙaci duk sassan biyu su fara janye makamai kwanaki biyu da fara aiki da shirin tsagaita wuta.