1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawaita cin jan-nama na haifar da cutar sankara

Suleiman BabayoOctober 26, 2015

Rage cin jan-nama da wanda aka sarrafa da sinadarai zai iya dakile cutar sankara.

https://p.dw.com/p/1GuYR
Rotes Fleisch
Hoto: picture-alliance/ dpa

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce bincike ya nuna akwai yuwuwar cin jan nama da nama wanda aka sarrafa da sinadarai masu hana abu lalace ka iya janyo cutar sankara, da ake kira cutar daji. Hukumar ta ce bayan bitar wasu bincike-bincike kimanin 800 an gano shaidar da ke danganta kamuwa da cutar sankara da cin jan-nama ko kuma nama da aka sarrafa da sinadarai da ke hana abu lalacewa da wuri. Amma idan mutum ba ya ci da yawa, babu wata illa.

Sannan binciken ya gano kimanin mutane dubu-34 ke mutuwa duk shekara saboda cutar sankara da ke da dangantaka da haka. Sai dai nama na tsintsaye kamar kaji saura gami da kifi ba a gano wata shaidar suna janyo cutar sankara ba.