1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan mace-mace a arewacin Najeriya

December 16, 2013

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane 1, 200 ne suka hallaka sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram, tun daga watan Mayu kawo yanzu.

https://p.dw.com/p/1AaiW
Hoto: AP

Tun dai daga ranar 14 ga watan Mayun da ya gabata ne, gwamnatin Najeriyar a karkashin jagorancin shugaban kasa Goodluck Jonathan ta kakaba dokar tabaci a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe dake yankin arewa maso gabashin kasar, tare kuma da tura dubban sojoji da jiragen yaki, a wani yunkuri da ta bayyana da na yaki da ta'addanci a yankin dake fama da rikici.

Rahoton da hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Duniya wato OCHA ta fitar dai, ya nunar da cewa a kallah mutane 1, 224 ne aka kashe tun daga sanya dokar ta baci a wadannan jihohi kawo yanzu. Wannan dai shine karo na farko da Majalisar Dinkin Duniyar ta bada rahoto kan adadin wadanda suka rasa rayukansu a wannan yanki sakamkon hare-haren da ke da nasaba da 'yan kungiyar Boko Haram, wadda ke yin gwagwarmaya da makamai a Tarayyar Najeriyar, tun bayan kaddamar da dokar ta baci a yankin na arewa maso gabashin kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu