1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko matakan Amirka za su kawo karshen rikicin Yemen?

Mahamud Yaya Azare LMJ
February 16, 2021

A daidai lokacin da dokar soke 'yan tawayen Huthi daga jerin kungiyoyin 'yan ta'adda da shugaban Amirka Joe Biden ya sanyawa hannu ke fara yin aiki, mayakan na Huthi sun tsananta hare-harensu kan Saudiyya.

https://p.dw.com/p/3pS6t
Yemen Huthi Kämpfer
Zafafan hare-hare kan Saudiyya daga mayakan Huthi Hoto: Hani Mohammed/AP Photo/picture-alliance

Bayan cire kungiyar ta mayakan Huthi daga cikin jerin kungiyoyin ta'adda da tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya sanya su, sabon shugaban Amirkan da ya cire su a jerin Joe Biden ya kara da tura jakadansa na musamman Linder Kings zuwa kasashen na Saudiyya da Yemen a  yunkurin da ya ce kasarsa na yi na kawo karshen yakin shekaru bakwai da ya daidaita kasar ta Yemen.

Karin Bayani: Yemen a shekaru 10 da juyin-juya halin Larabawa

Zafafa hare-haren da 'yan Huthin ke yi a daidai kan wannan gabar ciki har da wanda suka kai da jirage masu sarrafa kansu a filayen jiragaen sama na biranen Jeddah da Abha, ya janwo dasa ayar tambaya kan hakikanin manufar mayakan na Huthi da kuma irin tasirin da hakan zai yi ga matakin neman sasantawar da gwamnatin ta Biden ke ikirarin neman yi kan rikicin  na Yemen.
An dai jiyo kakakin fadar mulkin Amirkan, Ned Prince na yin tir da hare-haren da ya kira da baker aniya, to sai dai ya kara da shan alwashin cewa hakan ba zai sanya kasarsa ta canja aniyarta ta taimakon al'ummar Yemen fita daga mummunan halin da yakin da yaki ci yaki cinyewa ya sanya su ba. Sai dai a hannu guda Janar Abdulgani Zubaidi na 'yan Huthin, ya jaddada cewa da ma can Amirkan ita kadai ke kidanta take rawarta.

Der Jemen nach fünf Jahren Krieg
Hare-haren rundunar taron dangi karkashin Saudiyya, sun ragargaza YemenHoto: Hani Al-Ansi/dpa/picture alliance

Karin Bayani: Taron neman agajin kudin sake gina Yemen

Tuni dai Saudiyya ta nemi gwamnatin Biden da ta sake yin tunanin ta nutsu kan 'yan Huthin da ta ce ba 'yan goyo da zani ba ne. Dr Nashwa Dhirgam kwararriya ce kan siyasar Amirka a Gabas ta Tsakiya, ta fadawa gidan Talabijin na Al-hurrah cewa da biyu kan sababbin hare-haren na 'yan Huthi: "Zafaffa hare-haren Huthi kan Saudiyya, adaidai lokacin da baki dayan kashen duniya ke son ganin an kawo karshen yakin Yemen da sasanta rikicin nukiliyar Iran, wata babbar dama ce ga mayakan na Huthi su nuna cewa su ba kanwar lasa ba ce domin cimma yarjejeniya mafi riba garesu a Yemen, kuma uwar gijiyarsu Iran ta cimma muradunta kan dambarwar nukiliyarta."