1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yemen ta nemi agajin kasashen duniya

Abdul-raheem Hassan
September 21, 2017

Shugaban kasar Yemen Abd Rabu Mansour Hadi, ya kirayi hankalin saura kasashen duniya a yayin jawabinsa a zauren Majalisar Dinkin Duniya wajen kawo dauki ga yankunan kasar da ke hannun 'yan tawaye.

https://p.dw.com/p/2kUwt
Jemen Präsident Abed Rabbo Mansur Hadi
Hoto: Reuters/F. Al Nasser

Shugaba Hadi ya ce akwai bukatar Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashe su matsa kaimi wajen daukar matakai masu tsauri a kan 'yan tawayen Houthi, shugaban ya koka kan yadda mayakan Huthi suka yi patali da dukkanin wani yunkuri na sasanta tsakanin su da gwamnati inda ya zargi kasar Iran da ke mara musu baya wajen iza su aikata ba daidai ba.

A yanzu dai sama da farafen hula dubu 5,000 ne suka mutu, yayinda wasu akalla sama da dubu 8,000 suka jikkata tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta fara sanya idanu a kan rikicin kasar a shekara ta 2015.

To sai dai wasu bayanai na kungiyoyin da ke sa ido a kasar, na zargin dakarun kasar Saudiyya da ke marawa Yemen din baya da kashe akalla kashi 60 cikin dari na fararen hulan kasar a jerin haren-haren da suke kai wa ta sama.