1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 50 da juyin mulki a Yuganda

January 25, 2021

Shekaru 50 da suka gabata a ranar 25 ga watan Janairun 1971, sojoji karkashin jagorancin Idi Amin sun ka madafun iko a kasar Yuganda.

https://p.dw.com/p/3oNfj
50 Jahre Uganda
Tsohon shugaban mulkin kama-karya na Yuganda Idi AminHoto: Getty Images

Idi Amin dai ya kwashe shekaru takwas yana mulkin kama karya da kashe duk wanda ya yi kokarin sukarsa, inda dubban mutane suka mutu karkashin mulkin nasa. Tankokin yaki sun mamaye birnin Kampala fadar gwamnatin kasar Yugandan, inda shekara ta 1971 ta zama mafarin mulkin Idi Amin wanda ya kwace madafun ikon kasar da ke yankin gabashin Afirka. Sabon shugaban gwamnatin mulkin sojan yana zaune a bayan motar alfarma tare da rakiyar sojoji cikin tankokin yaki, inda mutane ke daga hannu suna jinjina masa. Mafarkin Idi Amin ya zama gaskiya kamar yadda yake cewa: "Ya zama gaskiya."

Idi Amin yana da garin jiki, wanda yake son rayuwa. Ya yi aiki a rundunar sojan Birtaniya lokacin mulkin mallaka, inda ya zama mai nuna rashin imani. Shi ne bakar fata na farko da ya zama hafsan soja daga Yuganda.

50 Jahre Uganda
Idi Amin na jagorantar sojojinsaHoto: Getty Images

Kuma ya kasance zakaran dambe a ajin masu matsakaicin nauyi na kusan tsawon shekaru 10, ba kuma ya nuna sassauci: "Ina son sanar da duk 'yan wasan dambe cewar, hanyar ba da tabbaci ga alkalin wasa wanda ba ya son ka ko kasarka, shi ne doke mutum kwab daya."

Karin Bayani: Tarihin Idi Amin Dada

Idi Amin ba ya nuna tausayi a fagen dambe haka lokacin da ya zama shugaban kasa. Ya fara mulkin da kashe mutane magoya bayan wanda ya gada da masana da alkalai gami da hafsoshin soja duka sun bace. Daga bisani an gano gawarwakinsu a cikin kogi mai shake da kadoji. Idi Amin yana jin dadin gana azaba ga mutane ta hanyar kisa, a cewar Kenneth Obong daraktan bangaren koyar da tarihi a jami'ar Nairobi da ke Kenya: "Ya iya gana azaba ga mutane da raunata su. Ya samo wannan dabara daga tsarin mulkin mallaka. Gana azaba domin samun iko. Haka yake tafiyar da rayuwarsa. Haka kuma lokacin da ya yi mulki."

Uganda Tansania Krieg 1979 Rebellen
Sojojin Tanzaniya sun yi nasara kan YugandaHoto: STF/AFP/Getty Images

Lokacin da mulkin ta'addancin ya kawo karshe a samu kayukan wasu masu adawa da shi a cikin na'urar sanyaya ruwa, firiji, da ke fadarsa. Kimanin mutane dubu-300 ya kashe a tsawon mulkin. A lokaci guda Idi Amin yana jan hankali.

Yana son yin iyo a cikin ruwa. Ana nuna shi lokacin da yake ziyartar gasar iyo a wani wajen linkaya da ke Otel-Otel da ke babban birnin kasar ta Yuganda. Duk lokacin da ya saki jiki wadanda suke gasa da shi sukan yi a hankali domin tabbatar da cewa ba su wuce shi ba.

Sojojin Tanzaniya sun karya lagonsa

Dan kama karya dole ya samu nasara ko wanda ya yi kasadar wuce shi ya fuskanci barazana. Daya daga cikin abubuwa da suka karya gwamnatin Idi Amin shi ne koma-bayan tattalin arziki. Galibin harkokin kasuwancin Yuganda na hannun 'yan Indiya da Pakistan da Turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka kai Yuganda. Shugaban kasar ya sallame su lokacin bazara a shekarar 1972, bayan mafarkin ranar hudu ga watan Agusta. Ana matsalar tattalin arzikin Idi Amin ya tura sojoji suka mamaye wani bangaren Tanzaniya a shekarar 1979, abin da ya sa dakarun Tanzaniya mayar da martanin da ya kawo karshen gwamnatin Idi Amin tare da tafiya gudun hijira Saudiyya, inda ya mutu a shekara ta 2003.