1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yukren: wani tsaiko da Yanukovych ke amfani da shi

January 30, 2014

Majalisar dokokin Yukren ta ba wa kanta lokaci na neman mafita daga dambarwar siyasar kasar. Ita kuma kungiyar EU ta dukufa wajen yin sulhu.

https://p.dw.com/p/1AzXO
Ukraine Parlamentssitzung 28.01.2014 Plenum
Hoto: picture-alliance/dpa

Ba zato ba tsammani a wannan Alhamis shugaban kasar Yukren Ukraine Viktor Yanukovych ya fara wani hutu na rashin lafiya, inda zai gusa daga rikicin da ke ci-gaba a kasarsa, bayan 'yan majalisa sun kasa cimma matsaya game da wata dokar yafiya ga masu zanga-zanga. Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da tarayyar Turai ke kokarin shiga tsakani don yin sulhu.

Rashin lafiyar da ya shafi numfashin shugaba Viktor Yanukovych na zaman wani sabon lamari a rikicin kasarsa da ya kai shi ga amincewa da murabus din Firaminista Mykola Asarov a wani mataki na kwantar da hankalin masu zanga-zanga.

Takaddama game da dokar afuwa

Ukraine Maidan in Kiew 25. Januar 2014
Masu bore: "sai mun ga abin da ya ture wa buzu nadi"Hoto: Getty Images

A ranar Laraba majalisar dokokin kasar ta Yukren, ta amince da dokar afuwa ga 'yan adawa da ke zanga-zanga, dokar kuma da aka gindaya mata sharadin cewa dole masu adawa da gwamnati su janye daga gine-ginen hukumomin kasar da suka mamaye. Da yawa daga 'yan hamayya sun nuna adawa da dokar, inda suka nuna bukatar sakin masu zanga-zangar ba da wani sharadi ba. A saboda haka suka yi kira ga masu zanga-zanga da ka da su janye daga kan tituna da kuma gine-ginen gwamnati. Vitali Klitschko daya ne daga cikin shugabannin 'yan adawar kasar.

"Wannan doka da aka amince da ita kamar sauran dokokin kasar, ba an yi ne saboda biyan bukatun jama'a ba. Kamar wata doka ce ta masu fashin teku a Somaliya , wadanda ke karbar kudin fansa kafin su saki mutanen da suka yi garkuwa da su."

Ba a hango mafita ba

Har yanzu ba alamar kawo karshen rikicin siyasar cikin hanzari, domin har wannan lokaci ba a tattauna game da babbar bukatar masu zanga-zangar ba wato shirya sabon zabe. Hakazalika za a dauki tsawon lokaci kafin yi wa kundin tsarin mulki canje-canje na wani sahihin tsarin demokradiyya. Shugaba Yanukovych na amfani da wannan jinkirin. Da shi da gwamnatinsa sun samu karin lokaci na daukar matakan shawo kan boren, watakila ma su yi amfani da karfin tuwo wajen tarwatsa su.

Ba tabbas ko 'yan adawar za su iya durkussar da gwamnati. Kowane bangare ya dage kan matsayinsa kamar yadda furucin Mikhailo Tschetschetov na jam'iyyar da ke kan mulki ya nunar.

"Kasar ta tsaya cak. Dambarwar siyasar ta tsayar da komai. Dole a mika wa ma'aikatan al'umma gine-ginen da aka mamaye, dole ne a janye daga dandalin 'yanci, dole kasar ta koma bakin aiki."

Ashton a birnin Kiev

Catherine Ashton Besuch in Kiew am 29.01.14
Ashton da Yanukovych a Kiev cikin watan Disamban 2013Hoto: Picture-Alliance/dpa

A dangane da wannan halin yanzu kungiyar tarayyar Turai ta karfafa yunkurin da take na sulhu. Bayan ziyarar da kwamishinan fadada kungiyar EU Stefan Füle ya kai Kiev babban birnin kasar ta Yukren, a ranar Laraba jami'ar harkokin wajen EU Catherine Ashton ta isa birnin, kwanaki biyu gabanin lokacin da aka shirya za ta fara wannan ziyara don tattaunawa da shugaban kasa da kuma wakilan 'yan adawa. A ra'ayinta dai tattaunawa ce kadai za ta kai ga magance rikicin.

"Na kadu da rahotannin da na ji game da halin da ake ciki. daya daga cikin muhimman abubuwan da muke bukatar mu tinkara shi ne hana tashe-tashen hankula da kuma tursawawa."

Duk da tsananin sanyin hunturu masu zanga-zanga a tsakiyar birnin Kiev sun ce za su ci-gaba da zaman dirshan har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi. Tun farkon wannan makon ba a yi wani taho-mu-gama tsakaninsu da 'yan sanda da suka yi musu kofar rago ba, sai dai lamarin ka iya canjawa a kowane lokaci.

Mawallafa: Roman Goncharenko / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu