1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin warware rikicin Mali

December 3, 2012

Blaise Compaore ya gana da tawagar gwamnatin ƙasar Mali

https://p.dw.com/p/16uvA
Blaise Compaore, President of Burkina Faso, gestures during a briefing at the climate summit in Copenhagen, Denmark, Thursday, Dec. 17, 2009. A Danish official says there is little hope for a comprehensive climate deal in Copenhagen because negotiations between rich and poor countries are deadlocked. (AP Photo/Anja Niedringhaus)
Blaise CompaoréHoto: AP

Shugaba Blaise Compaore na Burkia faso da ƙungiyar ECOWAS ta ɗorawa yaunin shiga tsakanin rikicin ƙasar Mali, ya gabatar da ajendar tattanawa tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa, da zumar cimma tudun dafawa.

A yayin da gamayyar ƙasa da ƙasa ke jan ƙafa wajen gano bakin zaren warware rikicin ƙasar Mali, mai shiga tsakanin wannan rikici, wato shugaba Blaise Compaore na Burkina Faso, na cigaba da ganawa da ɓangarori daban- daban.

Bayan tattanawa da wakilan ƙungiyoyin Ansar Dine da na MNLA, a ranar Lahadi ya haɗu da tawagar gwamnatin Bamako.

Amma Ag Mahmud shine ,shugaban Hulɗoɗi da ƙasashen ƙetare na ƙungiyar tawayen MNLA, kuma ya na daga cikin tawagar da ta gana da shugaba Blaise Compaore, ya baiyana tasiri wannan haɗuwa:

Burkina's President Blaise Compaore (C), Benin's President Boni Yayi (L) and Ivorian President Alassane Ouattara are pictured during an ECOWAS Summit gathering west African leaders to plot a military strategy to wrest control of northern Mali from Islamist groups as fears grow over the risks they pose to the region and beyond, on November 11, 2012 in Abuja. West African plans could see the mobilisation of some 5,500 soldiers, essentially but not totally drawn from the region. Between 200 and 400 European soldiers will train troops in Mali, according to the operational plan. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

"Wannan haɗuwa tamkar share fage ne na tattanawa ta zahiri,shugaba Blaise Compaore ya gabatar mana da Ajendar sa, sa-anan ko wace tawaga zata naɗa mambobin ta, sa-anan daga baya tawagogin biyu su haɗu su fara tattanawa".

Tawagar gwamnatin ƙasar Mali da ta halarci taro da shugaba Blaise Compaore, ta bada haɗin kai ga yunƙurin sulhunta rikicin cikin ruwan sanhi tare da ƙungiyoyin biyu da suka nuna shawar haka.

Kisima Gaku mashawarci ne ta fannin tsaro a ofishin Ministan Tsaron ƙasar Mali ga abinda shi kuma yake cewa

"Gamayyar ƙasa da ƙasa ta fito ƙarara ta ce tataunawar da za-a yi, ba zata hana a yi shirye-shiryen yaƙi ba. saboda haka idan za ayi tattaunawa ta gaskiya, to tilas mai shiga tsakani ya haɗu da tawagogin da zasu tattaunawa gaba da gaba."

A halin da ake cikin yanzu a ƙasar, har illa yau tana ƙasa tana dabo domin ƙungiyar Ansar Dine da ke riƙe da wani yanki na arewacin ƙasar ba ta nuna wata alama ba, ta janyewar dakarunta.

Saidai a na su gefe jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyin fararen hula da dama na ƙasar Mali, sun nuna adawa da hawa tebrin shawara da 'yan tawaye, wanda a tunaninsu mataki ne kawai na yaudara.

In this Thursday, Sept. 27, 2012 photo, Islamist commanders instruct 13-year-old fighter Abdullahi to man a pickup-mounted machine gun, during a meeting with an AP journalist, in Douentza, Mali. Islamists in northern Mali have recruited and paid for as many as 1,000 children from rural towns and villages devastated by poverty and hunger. The Associated Press spoke with four children and conducted several dozen interviews with residents and human rights officials. The interviews provide evidence that a new generation in what was long a moderate and stable Muslim nation is becoming radicalized, as the Islamists gather forces to fight a potential military intervention backed by the United Nations. (Foto:Baba Ahmed/AP/dapd)
Hoto: AP

A ƙarshen mako, shugaban riƙwon ƙwarya na ƙasar Mali Diyukunda Traoré ya kai ziyara aiki a jamhuriyar Nijar, inda ya gana da takwaransa Mahamadu Isufu.

Shugabanin biyu, sun yi masanyar ra'ayoyi game da hanyoyin warware rikicin Mali, sannan sun baiyana takaici game da yadda ake samun tafiyar hawainiya daga Majalisar Dinkin Duniya, wajen ɗaukar matakan soja kan ƙungiyoyin da suka mamaye yankin arewacin Mali, mussamman ma Alqida da MUJAO.

Mawallafiya: Mariam Mohammed Sissy
Edita: Zainab Mohammed Abubakar