1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsin lamba kan 'yan ta'adda tsakanin Faransa da G5 Sahel

Abdoulaye Mamane Amadou
July 1, 2020

Faransa da kasashen yankin Sahel sun aminta da kara matsa kaimi kan 'yan ta'adda biyo bayan gagarumar nasarar da suka bayyana samu kan masu da'awar da ke neman kaka gida a wasu iyakokin kasashen yankin.

https://p.dw.com/p/3ebgZ
Frankreich l Macron wirbt für Sahel-Initiative
Hoto: Reuters/G. Horcajuelo

A yayin wani taron kolinsu da suka kammala a yammacin jiya a birnin Nouakchott na Murtaniya, shugaba Emmaneul Macron ya ce sojan kasashen hadin gwiwa da takaransu na Faransa, sun fatattaki masu tayar da kayar bayan a wasu iyakokin Mali da Nijar da Burkina Faso, inda masu da'awar jihadin suka fi tsananta kai hare-hare a baya bayan nan tare da kwace sansanoninsu da dama, yana mai cewa wannan mataki zai ci gaba dorewa kana kuma za a kara adadin jam'an tsaro a makonin dake tafe domin rundunar hadin gwiwar kasashen da na Turai mai suna Takuba ta mamaye wuraren da aka karba a hannun 'yan ta'adda.