1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin sassanta tsakanin Anti Balaka da Seleka

July 11, 2014

'Yan kasar Jamhuriyar Afirka, sunyi barazanar kauracewa taron sasantawar da zai gudana a Kongo Brazzaville, inda suke bukatar kasancewar taron a kasarsu.

https://p.dw.com/p/1CbY1
Hoto: picture-alliance/dpa

A kalla wakilan jam'iyun siyasa 59, da kuma na manyan gungun addinan kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya guda uku ne, suka yi barazanar kauracewa taron tattaunawa, na neman sassanta 'yan kasar da zai gudana a ranar 21 ga watan nan na Yuli a kasar Kongo Brazzaville, inda sukayi kira ga Shugaban kasar ta Kongo Denis Sassou N'Guesso, da ke a matsayin mai shiga tsakani, da ya yi duk abun da ya dace na ganin ya shirya wannan haduwa cikin kasar su ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Burin dai da aka sa ma gaba kan wannan tattaunawa, shi ne na kawo 'yan kungiyar Anti-balaka, da na kungiyar Seleka, su rattaba hannu tare da kiran tsagaita wuta a wannan kasa.

Tuni dai bangarori uku, da suka hada da Kungiyar Tarayyar Afirka, da Majalisar Dinkin Duniya, da kuma Shugaba Sassou NGuesso, ke ci gaba da nazari a halin yanzu domin tantance sauran mutanen da ya dace su halarci wannan tattaunawa, wadanda ake ganin suna da wani fada a ji, abun da yake da wuyar samu a wannan kasa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba