1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Yunwa ta karu a kasar Mali

December 9, 2021

Kungiyoyin da ek bayar da agaji a Mali, sun ce karancin abinci na ci gaba da karuwa a kasar a wannan shekara. Hakan ya samo asali ne sakamakon matsalolin da kasar ke ciki.

https://p.dw.com/p/442j4
Frauen Burkina Faso
Hoto: APImages

Bayanai na nuna cewa ana ci gaba da samun karuwar wadanda ke fama da yunwa a kasar Mali.

Sabbin alkaluma sun una cewa adadin su ya karu da mutum miliyan daya da dubu 200 a bana.

Ana dai alakanta karuwar fama da karancin abincin ne a Mali da matsalolin tsaro da rashin kyawun damina da ma ta annobar corona.

Kungiyoyin agaji 22 da ke aikin jin kai a kasar ne dai suka ce hakan a wani rahoto da suka fitar.

Tuni ma dai mutum dubu 400 suka tsere daga kasar, inda farashin abinci ke ci gaba karuwa a kullum rana ta Allah.

Fari kuma ya lalata sama da hekta dubu 225 ta filayen noma.

Kungiyoyin na agaji, na cewa hare-haren 'yan bindiga na hana su iya kai dauki a yankunan da matsalar ta fi kamari a Malin.