1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen gama gari a Saliyo cike da ƙalubale

November 17, 2012

Zaɓen na zaman zakaran gwajin dafi ga ƙasar da ta yi fama da shekaru goma na yaƙin basasa da ya hadasa mutuwar mutane dubu 120

https://p.dw.com/p/16kyC
A woman casts her ballot during presidential elections in Freetown, Sierra Leone November 17, 2012. Sierra Leoneans vote on Saturday in elections they hope can propel the small West African state into an era of prosperity based on mining and oil after a decade of difficult recovery from civil war. The presidential and parliamentary polls, the third held since the end of the 1991-2002 conflict, pit President Ernest Bai Koroma and his ruling All People's Congress (APC) against challenger Julius Maada Bio, a former junta leader who represents the Sierra Leone People's Party (SLPP). REUTERS/Joe Penny (SIERRA LEONE - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

 Al'umma na kaɗa ƙuria a zaɓen gama garin da ake gudanar wa a ƙasar Saliyo, inda kimani mutane miliyion biyu da rabi wanda suka cancanci zaɓe zasu zabi shugaban ƙasa da wakilan yan majalisu dokoki  da kuma na ƙananan hukumomi.

Masu aiko da rahotanin sun ce ko'ina a cikin birnin Freetown babban birnin ƙasar jama'a sun ja dogon layi a  bakin runfunan kaɗa ƙuria.Zaɓen wanda wani zakaran gwanji dafi ne na dimokaradiyya ga ƙasar da ta yi fama da yaƙin basasa na kusan shekarun goma.

Yan takara guda tara ne zasu fafata   a ciki hada shugaban mai barin gado Ernest koroma wanda ke kan mulki tun shekarun 2007.Masu  lura da  al'amura  yau da gobe na cewar ba mammaki ɗan takarar jam'iyyun siyasar na addawa Julius Maada  Bio ya taka rawar gani , ko da shi kema ma  ana hasashe cewa Koroman shi ne zai lashe zaɓen.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane

Edita      :  Umaru Aliyu