1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Za a ci gaba da tsare Sowere

Uwais Abubakar Idris RGB
August 8, 2019

Wata babban kotun Abuja ta amince da bukatar hukumar tsaro ta farin kaya DSS, kan ci gaba da tsare jagoran masu zanga-zangar juyin juya hali Omeyele Sowere

https://p.dw.com/p/3NaKY
Nigeria Omoyele Sowore
Hoto: CC by M. Nanabhay

A safiyar wannan Alhamis, kotun da ke tsakiyar birnin Abuja ta cika makil da jama’a domin wannan shari’a a karkashin jagoranci Alkali Taiwo Taiwo wanda ya dauki dogon lokaci yana karanta  bayanai na takardun shaida da lauyoyin da ke  tuhumar wanda ake zargi suka gabatar masa, takardun da ke dauke da bayanai na irin laifufukan da suke zargi Mr Sowere da aikatawa, abinda yasa suka yi amfani da dokar yaki da aiyyukan ta’adanci ta Najeriya don neman izinin kotun, kan ci gaba da tsare shi.

'Yan sanda a lokacin da suke kokarin kama masu goyon bayan juyin juya hali
'Yan sanda a lokacin da suke kokarin kama masu goyon bayan juyin juya haliHoto: Reuters/Str


Mai shari’a Taiwo Taiwo da ya bada misali da sashi na 27 da tsarin mulkin Najeriyar bisa wannan bukata, to sai dai yace dalilan da hukumar tsaro ta farin kayan ta bayar na zargin Sowere da aikata ta’adanci, ta hanyar kokarin tayar da rikici wanda zai iya yiwuwar  tarwatsa yanayin zaman lafiyar jama’a , ya ce, a shari’a kalma ce mai harshen damo, laifin dai na nan a matsayin zargi, don haka ya amince hukumar ta ci gaba da tsare shi na tsawon kwanaki 45 farawa daga wannan Alhamis zuwa 21 ga watan Satumba mai zuwa.


Har zuwa wannan lokaci dai,  ba’a gabatar da Mr Sowere a gaban kotu ba balle a yi maganar fara shari’ar. Tuni masu fafutukar ta neman juyin juya hali  suka maida martani tare da cewa ba su yarda da wannan hukunci ba. A yayin da kungiyoyin kare hakkin jama’a ke ci gaba da Allah wadai da kame masu zanga-zangar juyin juya hali a kasar, ita kuma gwamnati na yabawa wadanda suka yi watsi da kiran.