1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar fitar da hatsin Ukraine

Zainab Mohammed Abubakar
July 22, 2022

Rasha da Ukraine sun sanya hannu kan yarjejeniya mai muhimmanci na sake bude tashar jiragen ruwan Ukraine na Bahar-Maliya domin jigilar hatsi zuwa kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/4EWX2
Ukraine-Krieg | Abkommen über Export von ukrainischem Getreide
Hoto: OZAN KOSE/AFP

Wannan yarjejeniya ta haifar da fatan kawo karshen barazanar karancin abinci da duniya ke fuskanta sakamakon mamayen da Rasha ta yi wa makwabciyarta Ukraine.

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya kasa boye farin cikinsa dangane da wannan sabon shafi na fatan ceto duniya daga halin karancin cimaka tare da yaba wa bangarorin biyu.

"Kun shawo kan matsalolin tare da ajiye bambance-bambancenku a gefe don share fagen samar da wani shiri wanda zai dace da moriyar jama'a baki daya, inganta jin dadin bil'adama shi ne ginshikin wannan tattaunawar, tambayar ba ta kasance meye alheri ga wani bangare ko kuma wani ba. An mayar da hankali ne kan abin da ya fi muhimmanci ga al'ummar duniyarmu."

Yarjejeniyar dai na zama kololuwar tattaunawar shiga tsakani na watanni biyu da MDD da Turkiyyar da ke da wakilci a kungiyar tsaro ta NATO kuma kasar da ke da kyakkyawar alaka da Rasha da Ukraine suka jagoranta.