1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a rantsar da Mohammadu Buhari

Abdourahamane HassaneMay 29, 2015

Wannan biki na rantsar da sabon shugaban Najeriyar na zuwa ne a dai dai lokacin da ƙasar ke fama da matsaloli na tattalin arziki

https://p.dw.com/p/1FYaY
Nigeria Wahlkampf Mohammadu Buhari & Yemi Osinbajo
Hoto: picture-alliance/dpa

Nan gaba a yau aka shirya ƙaddamar da bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Najeriya Mohammadu Buhari,bayan nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a cikin watan Maris da ya gabata a gaban shugaban mai bari gado Goodlluck Jonathan.

An shirya shugabannin daga ƙasashen Yankin Afirka da Turai da Asiya da kuma na manyan ƙungiyoyi za su halarci bikin.