1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a sake kirga kuri'u a Saliyo

March 13, 2018

Hukumar zabe a Saliyo ta ce za ta sake kidaya kuri'un wasu daga cikin runfunan zabe.

https://p.dw.com/p/2uFNB
Wahlen in Sierra Leone  2018
Hoto: DW/A.-B. Jalloh

Hukumar zaben kasar Saliyo ta ce zata sake kidaya kuri'un wasu daga cikin runfunan zabe, dai dai lokacin da sakamakon farko ke nuna dan takarar jam'iyyar adawa Julius Maada Bio a kan gaba. Shugaban hukumar zaben kasar Mohammed Alie Conteh, ya ce runfuna 154 za a sake lissafa kuri'un nasu.

Shi dai dan takaran na adawa na da kashi 43.3 cikin dari daga kashi 75 na kuri'un da aka lasafta, yayin da dan takaran jam'iyya mai mulki Samura Kamara ke da kashi 42.5. Mutane miliyan uku da dubu goma sha takwas ne aka yi wa rajista a fadin kasar ta Saliyo.

Alamu kuma na nua yiwuwar zuwa zagaye na biyu a zaben na ranar 7 ga wannan watan na Maris, saboda gaza samun kashi 55 na kuri'un da zai kai dan takara ga nasara, a zagayen na farko.