1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a saki dan jaridar da aka kama a Masar

June 16, 2014

Rahotanni daga Masar na cewar an bada umarnin sakin dan jaridar na Al-Jazeera da ke yajin cin abinci bayan da aka tsare shi ba tare da yi masa shari'a ba.

https://p.dw.com/p/1CJT6
Wasu 'yan jarida da ke zanga-zanga a Masar saboda kame abokan aikinsu
Hoto: picture-alliance/dpa

Babban mai gabatar da kara ba Masar ya bada umarnin sakin Abdullah Al-Shamy, dan jaridar nan na Al-Jazeera da ya shafe kwanaki 130 ya na yajin cin abinci don nuna rashin amincewa da tsare shin da ake yi ba tare da shari'a ba. Wata sanarwa da aka fidda kan sakin na Al-Shamy ta ce an yanke shawarar sallamarsa ne da wasu mutane 13 saboda rashin koshin lafiya da suke fama da ita.

A cikin watan Agustan da ya gabata ne dai aka tsare dan jaridar da takwarorinsa bisa zargin kasancewarsu 'yan kungiyar nan ta 'yan Uwa Musulmi ta Shugaba Muhammad Morsi da ma taimaka musu wajen yi wa gwamnatin kasar zagon kasa, zargin da Al-Sahmy din da abokan aikinsa suka musanta.

Kasashen duniya da dama kafofin watsa labarai a duniya sun yi sukar lamirin gwamnatin Masar na tsare 'yan jaridar da ma gaza gabatar da wasunsu gaban kuliya domin yi mu shari'a, lamarin da ake gani tamkar tauye hakkin 'yancin fadin albarkacin baki ne.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman