1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za´a ci-gaba da shawarwarin kafa gwamnatin Falasdinawa a Damascus

January 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuTo
Bisa ga dukkan alamu za´a ci-gaba da tattaunawa tsakanin shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da jagoran Hamas Khaled Mashaal a birnin Damascus, da nufin kafa wata gwamnatin hadin kan kasa. Dukkan bangarorin biyu sun ce za´a ci-gaba da shawarwarin bayan kai-komo da jami´an diplomasiyan Syria suka yi. da farko wani babban jami´in Hamas ya ce taron wanda aka dage yin sa a jiya asabar, ba za´a yi shi ba gaba daya. Yanzu haka dai Abbas na birnin Damascus inda ya ganawa da jami´an Syria.