1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za'a je zagaye na biyu a zaben kasar Brazil

October 6, 2014

Yanzu dai ta tabbata cewa Shugaba Dilma Rousseff ce da Aecio Neves, zasu fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Brazil a ran 26 ga watan Octoba.

https://p.dw.com/p/1DQCI
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff, da ke neman wa'adi na biyu ta kasance kan gaba da kashi 41,6 cikin 100, yayin da Aecio Neves ya zo na biyu da kashi 33,6 cikin dari, sannan Marina Silva da ake zaton za ta zo ta biyu, ta zo ta uku da kashi 21,3 cikin 100. A ranar 26 ga watan nan na Octoba ne dai za'a je zagaye na biyu na wannan zabe, sai dai kawo yanzu 'yar takarar da ta zo ta uku bata fara zaben bengaran da zata marawa baya ba.

Tuni dai wanda ya zo na biyu a wannan zabe, Aecio Neves ya fara zawarcin 'yar takarar da ta zo ta uku Marina Silva na ganin ko za su gama karfi da karfe su fafa da shugabar mai ci a zagaye na biyu. Fiye da kashi 60 cikin 100 na magoya bayan Yar takara Marina Silva dai, tun farko sun sha alwashin goya ma Aecio Neves baya idan har yazo na biyu a wannan zabe.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba