Za'a kafa gwamnatin Hadaka a Izraela
March 15, 2013Gabanin cikar wa'adin da aka debar masa, da ziyara mai cike da tarihi ta shugaban Amurka Barack Obama a yankin gabas ta tsakiya, priministan Izraela Benjamin Netanyahu, ya rattaba hannu akan yarjejeniyar kafa sabuwar gwamanatin hadaka da manyan abokan gamayyarsa. Jam'iyyar Netanyahu ta Likud da ta tsohon ministan harkokin waje Avigdor Lieberman, sun kasance cikin tattaunawar kwanaki 40 da jam'iyyar masu ra'ayin gurguzu, wadda keda mafi yawan kujeru a majalisar Izraelar mai wakilai 120. Sanarwar data fito daga fadar gwamnati na cewar, priministan yayi maraba da cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa tsakanin jam'iyyarsa ta Likud da Yisrael Beitenu da Yesh Atid da wadda ake kira Jewish Home. A wannan asabar ce, ake saran Priminista zai shaida wa shugaban kasa Shimon Peres cewar, ya sauke nauyin daya dora masa na kafa gwamnati, inda acewarsa zasu hada kai da aiki tare domin cigaban al'ummar Izraela.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Yahouza Sadissou Madobi