1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za´a turawa al´umar Falasdinawa taimakon kudi kai tsaye

June 17, 2006
https://p.dw.com/p/Butg
Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta ce bangarorin hudu dake tattauna batun samar da zaman lafiyar yankin GTT sun kusa cimma yarjejeniya kan yadda za´a tura taimakon gaggawa ga al´umar Falasdinu. A lokacin da take magana a Washington Rice ta ce Amirka da Rasha da KTT da kuma MDD na cikin shirye shiryen karshe na amincewa da wata shawara da kungiyar EU ta bayar na tura kudade kai tsaye ga al´umar Falasdinu ba tare da kudaden sun shiga hannun gwamnatin Hamas ba. Amirka da kungiyar EU sun saka sunan Hamas a jerin kungiyoyin ´yan ta´adda a duniya. Suna son kungiyar ta yi watsi da tashe tashen hankula kana kuma ta amince da Isra´ila.