1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za'a yiwa yarjejeniyar Schengen gyaran fuska

April 10, 2013

Kasashen Turai dake aiki da yarjejeniyar yancin shigi da fici ta Schengen sun sanar da shirin sake mata sabon tsari domin tsananta matakan tsaro a tsakaninsu

https://p.dw.com/p/18CzH
Hoto: picture alliance/Romain Fellens

A shekara ta 1995, kasashen kungiyar hadin kan Turai suka fara aiki da wata yarjejeniya da suka sanya mata sunan yarjejeniyar Schengen. Dukkanin kasashen kungiyar suna cikin wannan yarjejeniya, in banda Ingila da Ireland da Cyprus da Romania dakuma Bulgaria. Suma kasashen Norway da Iceland da Switzerland ko da shike ba wakilai bane a cikin kuingiyar amma suna mutunta yarjejniyar ta Schengen. A Karkashin wannan yarjejeniya jama'a suna da yancin shigi da fici ko da yake ma ana gudanar da bincikke akan iyakokinsu

A yunkurin kara tabbatar da tsaro a iyakokin nasu, wadannan kasashe a shekaru na casa'in sun bullo da wata cibiya ta musayar bayanai bisa manufar farautar masu aikata manyan laifuka, wadda aka sanya mata sunan cibiyar tara bayanai ta Schengen, ko kuma SIS a takaice. Yanzu dai za'a yiwa wannan cibiya gyaran fuska yadda hukumomi a kasashen na Turai zasu rika samun bayanan da suke bukata cikin gaggawa. Lokacin da aka kafa cibiyar da farko ta kunshi bayanai ne a game da mutanen da ake farautar su, ko dai saboda dalilai na aikata manyan laifuka ko kuma wadanda suka bace ana neman su ko kuma wadanda ya zama wajibi a lura da take-taken su na yau da kullum. Bayan da aka dauki sabbin kasashe a kungiyar ta hadin kan Turai, an fadada aiyukan da cibiyar take gudanarwa, abin da ya hada da bayanan hotunan fuskokin jama'a da hotunan yatsu, wadda a sakamakon haka, hukumomin shigi da fici da na kwasta da hukumomin shari'a ba ma suna samun damar binciken mutanen da ake nemansu saboda dalilai, misali na aikata manyan laifuka bane, amma har zasu iya farautar kayaiyaki, kamar motoci da makamai. Markus Beyer-Pollok na ma'aikatar cikin gida ta Jamus yace yana da muhimmanci kasashen dake karkashin yarjejeniyar ta Schengen su kara tsananta musayar bayanai tsakanin su, su kuma sami hanyoyi na bai-daya a game da yaki da aikata miyagun laifuka, bayan da aka kawar da bincike aiyakokin nasu na cikin gida.

Shi kuwa kakakin gwamnatin taraiya a fannin kare bayanan asiri na jama'a, Peter Schaar, yace:

"Musayar bayanai da labarai tsakanin kasashen na Turai ba wani sabon abu bane. Amma a sakamakon shiga mataki na biyu na tsarin musayar bayanan karkashin yarjejeniyar Schengen, ana bukatar cibiya da zata hade aiyukan hukumomin na Turai gaba daya a bangaren tara labarai da kare sirrin jama'a. Dangane da haka, hukumar kungiyar hadinkan Turai ta gabatar da tsarin yadda take ganin za'a cimma nasara ko da shike wannan tsari da ta gabatar har yanzu ana muhawara mai tsanani a kansa. Wasu kasashe suna ganin hukumar tana yi masu katsalandan a fannin kare sirrin yan kasa, sa'annan a bangaren masu da'awar hana tara bayanan jama'a suna korafin cewar hukumar ta wuce gona da iri. Wasu kuma suna cewar matakan kare sirrin jama'a da hukumar ta gabatar bai kai yadda misali, kotun kare kundin tsarin mulkin Jamus ta yanke hukunci a kansa ba. Kotun ta kololuwa ya nunar da cewar duk wnai mataki da za'a gabatar a game da tara bayanai kan jama'a da kuma kare su, tilas ya dace da bukatun kasar ta Jamus."

Kakakion ma'aikatar cikin gida, Markus Beyer-Pollok yace bayanan da ake tarawa basu wuce wadanda yan sanda suka gabatar ba, wadanda kuma su kansu suke bukata domin tafiyar da aiyukan su na binciken masu aikata manyan laifuka. Peter Schaar, kakakin gwamnatin taraiya a fannin kare bayanan jamja'a yace:

Peter Schaar
Peter Schaar wakilin gwamnatin Jamus a fannin kare sirrin jama'aHoto: dapd

"Abu mai muhimmanci shine shine a san irin bayanan da aka tara da kuma dalilin da ya sanya a aka tara su ko ake bukatarsu, suwanene suke da iko da kuma samun damar amfani da wadannan bayanai da aka tara, kuma wace dangantaka ke akwai tsakanin cibiyar da tara bayanai da sauran bukatu na kasashen kungiyar Schengen tattare da tsaro. A game da hakan, ana bukatar karin hadin kai da shawarwari yadda ba za'a turawa wata cibiya ko hukumar karfin iko ita kadai ba abin da zai zama illa ga mazauna kasashen na Schengen. A ganina, ana bukatar cikakken bayani game da haka."

Yanzu haka cibiyar ta tara bayanai, a bayan labarai na masu aikata manyan laifuka, takan kuma kungiya bayanan masu shigi da fici a ioyakokin cikin gida na kasashen Schengen. Ana kuma shirin fadada aiyukanta yadda zasu hade da bayanai Visa wato izinin shiga kasashen na Schengen.

Mawallafi: Pabst/Umaru Aliyu
Edita: Mouhamadou Awal