1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe a Congo

July 30, 2006

Yau an gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki a jamhuriyar democradiyar Congo

https://p.dw.com/p/Btyp
Shugaban rikon kwarya na Congo, Joseph Kabila yana kada kuri'ar sa
Shugaban rikon kwarya na Congo, Joseph Kabila yana kada kuri'ar saHoto: AP

To dama dai akan ce wai rana dai bata karya, sai dai uwar diya taji kunya. Al’ummar kasar Congo yau sun fito kwan su da kwarkwatan su domin kada kueri’u, karon farko a tsawon zamanin da mafi yawan yan kasar basa iya tunawa, domin zaben shugabamn kasa da sabuwar majalisar dokoki. Zaben na Congo da aka yi yau, shine na farko a wnanan kasa tsawon shekaru arba’in da shidda, kuma an yi shi ne tare da fatan zai kafa tushen kawo karshen tashin kankali da klashe kashe da yakin basasa da kasar tayi fama dasu tsawon wadannan shekaru. Gaba daya dai yan takara talatin da biyu ne suka shiga zaben na shugaban kasa, yayin da wasu mutane kimanin dubu goma suke takarar neman kujeru dari biyar a majalisar dokokin kasar

Tun kafin zaben na yau, an gudanar da kampe mai tsanani, inda yan adawa suka zargi gwamnati da laifin neman hana su taka wata rawar azo a gani a wnanan zabe. Dangane da haka ne, dan adawar da yafi suna a kasar ta Congo, wato Etienne Tschisekedi na jam’iyar UDPS ya kauracewa zaben, inda ya baiyana imanin cewar ko an kada ikuri’un ta hanyar gaskiya, ko an yi magudi, shugaban kasa na wucin gadi, Joseph Kabila ne zai sami nasara.

A hakika kuwa, masana da yan kallo masu tarin yawa sun baiyana imanin cewar Kabila ne zai lashe wnanan zabe, musmaman saboda rarrabuwa tsakanin yan adawa da suka tsaya takara dashi a zaben na yau. Dan takarar da ake zaton zai kalubalanci Kabila a zaben, shine Jean Pierre Bemba, tsohon dan tawaye, wanda yanzu yake rike da kmukamin mataimakin shugaban kasa.

Ko da shike zaben an tafiyar da mafi yawan sa lami lafiya, amma rahotani sun kuma yi nuni da tashe-tashen hankula a wurare da dama, kamar dai a yankin gabashin Congo, mai arzikin ma’adinai, inda aka kone wasu wuraren kada kuri’u. Kazalika, magajin garin daya daga cikin garuruwan yankin na gabasdhin Colngo, yace mutane ukku aka jiwa rauni, lokacin da matasa sukai kokarin hana kada kuri’u a wnanan yanki. Magajin garin Mbuyi-Maji yace wannan yanki ne da mazaunan sa suke goyon bayan shugaban yan adawa, Etienne Tschisekedi.

Yankin da yan adawa suka mamaye shi, kusa da kann iyaka, tsakanin Rwanda da Uganda, yana da muhimmanci a game da nasara ko rashinnasarar zaben gaba daya. Wadanda suka shaidar da zabe a wnanan yanki suka ce dimbin mutane da suka fita domin kada kuri’in su, sun maida zaben kamar dai wani gagarumin biki ne da aka asaba gani a rtanakun kasuwa a yankin. Gaba daya tashoshin zabe kimanin dubu hamsin ne suka shaidar da cincirindon masu kada kuri’u, kafin a kawo karshen zaben da misalin karfe hudu, agogon Nijeriya.

Zaben na yau an gudanar dashi ne karkashin matakan tsaro masu trsananin gaske. Majalisar dionkin duniya tana da sojojin ta kimanin dubu goma sha bakwai a kasar ta Congo, yayin da kungiyar hadin kann Turai ta aika da sojoji dubu guda zuwa kasar, domin tabbatar da tsaro da kuma ganin an gudanar da zaben ba tare da wani hargitsi mai yawa ba. Hukumar zabe mai zaman kanta tace sakamakon zaben na shugaban kasa za’a same shi ne nan da misalin makonni ukku masu zuwa, yayin da za’a sanar da sakamakon zaben kujeru dari biyar na majalisar dokokin kasar ta CFongo, idan aka kammala tara sakamakon da ya samu daga jihohi da lardunan kasar dabam dabam.