1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus sun mayar da hankali kan zaben Afirka ta Kudu

Mohammad Nasiru Awal SB
May 10, 2019

Zaben 'yan majalisar dokoki da ya gudana a Afirka ta Kudu ya dauki hankalin jaridun Jamus. Kana rundunar soji Jamus ta Bundeswehr na horas da sojojin Jamhuriyar Nijar ba tare da wata doka daga majalisar dokokin Jamus ba.

https://p.dw.com/p/3IIEE
Südafrika Parlamentswahl Stimmauszählung
Hoto: Reuters/R. Ward

A sharhin da ta rubuta a kan zaben jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce shugaban kasa Cyril Ramaphosa na bukatar gagarumin rinjaye a zaben idan ba haka ba to alkiblarsa ta neman yin sauye-sauye a kasar na cikin hatsari. Jaridar ta ce tun gabanin zaben shugaban ya sama cewa kasar matsalolin tabarbarewar tattalin arzikin da cin hanci da rashawa sun sa yarda da duk fata da al'umma ke da su sun yi rauni. Saboda haka shugaban ya ce yanzu lokacin yafiya da rashin hukunta masu laifi ya wuce, ya ce za a shiga zamanin ya zama dole a aiwatar da hukunci ga duk wanda aka samu da laifin cin hanci da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati.

Südafrika - Wahl / Präsident Cyril Ramaphosa
Hoto: picture-alliance/B. Curtis

Ita ma a sharhin da ta rubuta dangane da zaben na Afirka ta Kudu jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi mako guda gabanin zaben majalisar dokokin an shiga rashin tabbas a kasuwannin hada-hadar kudi na Afirka ta Kudu, kasar da ke ka gaba wajen karfin tattalin arziki a Afirka. Ta ce yayin da akasarin masu sayen hannun jari ke fatan jam'iyyar ANC da ke mulki za ta ci zaben kai tsaye, akwai shakku ko Shugaba Ramaphosa zai iya aiwatar da shirinsa na sauye-sauye. Jaridar ta ce dole shugaban wanda ya gaji Jacob Zuma, bayan ya yi murabus sakamakon jerin ababan kunya na cin hanci da rashawa a cikin watan Fabrairun 2018, sai ya yi da kyar kafin ya iya kawar da adawar da yake fuskanta a cikin jam'iyyarsa ta ANC.

Kongo| Ebola
Hoto: picture-alliance/dpa/Al-Hadji Kudra Maliro

Sojojin sa kai a Kwango na son su yaki Ebola da makamai wannan shi ne labarin da jaridar Die Tageszeitung ta buga tana mai mayar da hankali da ayyukan kungiyoyi masu daukar makamai a gabshin Kwango da ke yawaita kai hari a cibiyoyin yaki da anobar Ebola da ke a garin Butembo a gabashin Janhuriyar Demukurdiyyar Kwango. Jaridar ta ce 'yan bindiga na kungiyar Mai-Mai sun addabi mazauna garin musamman ma'aikatan kiwon lafiya da ke a cibiyar yaki da Ebola, inda a watan Afrilu suka hallak wani likita dan kasar Kamaru. Hakan na kawo babban koma baya a yaki da cutar wanda alkalumman da ma'aikatar kiwon lafiya ta Kwango ta bayar a baya-bayan suka nuna cewa a Butembo kadai mutum 175 suka rasu sakamakon sake bullar cutar watanni kalilan da suka wuce.

Niger Besuch Angela Merkel mit Präsident Mahamadou Issoufou in Niamey
Hoto: DW/S. Boukari

Jaridar Süddeutsce Zeitung ta leka Jamhuriyar Nijar tana mai cewa rundunar soji Jamus ta Bundeswehr na horas da sojojin Nijar ba tare da wata doka daga majalisar dokokin Jamus ba. Ko da yake ma'aikatar tsaro ta kare matakin da cewa sojojin na aiki ne karkashin aikin da rundunar ke yi a Nijar saboda haka ba sa bukatar amintar majalisar dokokin. Za ku ma sanar da majalisar dalilin da ya sa ba ta bukatar amincewar majalisar kafin ta yi wannan aiki. Kimanin sojojin kundubala na Jamus 20 ne ke aikin horas da takwarorinsu na Jamhuriyar Nijar.