1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben fidda gwani a jihar Zamfara ya gagara

October 1, 2018

A can ma jihar Legas Kudu maso Yammacin na Najeriya zaben na fidda gwani a APC mai mulkin ya ci tura inda aka dage zaben sai a ranar Talata bayan takaddama tsakanin jiga-jigai na jam'iyyar a jihar.

https://p.dw.com/p/35pq1
Nigeria, Wählerin mit Wählerkarte
Hoto: AFP/Getty Images/P. Utomi Ekpei

A jihar Zamfara Arewa maso Yammacin Najeriya zaben na fidda dan takarar gwamna na jam'iyar APC na ci gaba da fuskantar tarnaki sakamakon nuku-nuku gami da jan kafa da ake wajen gudanar da zaben, har kawo yanzu ba a bayyana yadda zaben zai gudana ba wanda hakan ya sa al'umma gudanar da zanga-zanga garuruwa dabam-dabam. Tin karfe 6 na safe masu kada kuri'a su kai dafifi dan gudanar da zabe amma dai zaben bai yiwuba sai ranar Talata a cewar jami'in jagoran kwamitin na APC a mataki na kasa Abubakar A. Fari. A can ma jihar Legas Kudu maso Yammacin na Najeriya zaben na fidda gwani a APC ya ci tura inda aka dage sai a ranar Talata sakamakon takaddama tsakanin gwamna mai ci da mai gidansa.