1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben fidda gwani na PDP ya bar baya da kura

Ubale MusaDecember 9, 2014

Jam'iyyar PDP mai mulki dai na fuskantar kalubale sakamakon rudanin da ya dabaibaye zabukan, da kan iya shafar tasirinta a zabukan shekara ta 2015 da ke tafe.

https://p.dw.com/p/1E1UR
Alhaji Adamu MUaazu wird neuer PDP Präsident
Hoto: DW/U.Musa

A Ebonyi an kare tare da sauyin shekar gwamnan zuwa Jam'iyyar Labour, sai dai makwabciyarta ta Enugu da ta kare tare da 'yan takara biyu da ke ikirarin dagawa jam'iyyar tuta a zaben gwamnan da ke tafe.

Banda Legas da ta kai har ga harbe-harbe na bindiga, sannan da can ma Katsina da 'ya'yanta ke fadin kotu ka raba, duk dai a cikin jamiyyar PDP mai mulkin Najeriya da ta kare zaben fidda gwanin da zai tsaya mata gwamna cikin jihohin kasar 36 a cikin rudani.

Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Tuni dai dama ta fara alamar yin baki da karin muni a cikin PDP da a kalla mako guda da tarukan fidda gwanin ta share tsawon kusan mako guda tana kokarin sulhunta rassan jihohin kasar daban daban da ke rikicin bako-da-dan gari da ma dan halal dame ikirarin yazo cirani.

Kafin daga baya a bude fagen famar tare da fuskantar mummunan rikicin da wasu ke yiwa kallon alamu na irin kalubalen da ke gaban jam'iyyar da ke tsaka mai wuya.

PDP da a wannan Larabar ke shirin tabbatar da shugaban da ke ci yanzu a matsayin mutumin da zai ja ragamarta a kokarin cigaban babakere ga fagen siyasar da ta dauki lokaci tana fada ana sauraro dai, daga dukkan alamu tana fuskantar babban taskun sassanta tsakanin 'ya'yanta cikin kasa da watanni biyun da ke tafe.

Nigerianischer Präsident Goodluck Jonathan 11.11.2014
Shugaba Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/AP

To sai dai kuma a fadar Dr Umar Ardo da ke zaman dan jam'iyyar kuma mai nazari a cikin harkokinta, sabbabin rigingimun nama iya kai jam'iyyar asarar damar samun gwamnonin a jihohi daban daban na kasar a halin yanzu.

Abun jira a gani dai na zaman tasirin sabbabin matakin ga jam'iyyar da ke kokarin hade kanta wuri gudu da nufin kauce wa barazanar jin kunya a wajen 'yan kanne.