1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben kasar Zimbabwe

Uwaisu Abubakar IdrisMarch 30, 2005

Ana ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zabe a kasar Zimbabwe, ko da yake A murika da kungiyar tarayyar Turai sun ce tsarin da aka yi wasan yara ne.

https://p.dw.com/p/Bvcd
Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe.
Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe.Hoto: AP

To a yanzu dai kam ana cikin jajibarin shiga zaben yan majalisun dokokin kasar Zimbabwen ne, wanda za’a yi a gobe alhamis idan Allah ya kaimu, lokacin da alummar kasar zasu zabi sabbin yan majalisun dokokin kasar 120.

Shugaban kasar Robbert Mugabe ya kwashi makw3ani yana karade sassan kasar inda yake yakin neman zabe a jamiyyarsa ta ZANU-PF a kokarin da yake da kara jadadda mulkinta na shekaru 25, Mr Mugabe na amfani da sabaninsa da Frym ministan Britaniya Tony Blair wajen yakin neman zabe, inda yake zarge Blair da cewar yana goyon bayan jamiyyar yan adawa ta MDC ce da nufin sake mulkin malaka a kasar.

To sai dai shugaban jamiyyar ta MDC Morgan Tsivangirai bai saurara mashi ba, ya mayar da murtani mai zafi, yana cewar ai yakin neman zabe ba wai maganar Frym ministan Birtaniya bane, magana ita ce samar da abinci da dubban al‘ummar Zimbabwe da ke cikin balain yunwa, ga matsanacin rashin aikin yi, Tsivangirai yace wadanan sune muhimman abubuwan da aka sanya a gaba a kasar da ta kwashe shekaru 25 da samun yancin da a lokacin tatalimn arzikin kasar ke bunkasa.

Abin farin ciki shine an gudanar da yakin neman zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da zub da jini ba, ba kaman na shekara ta 2000 da 2002 ba, inda aka raunata mutane da dama, wasu suka rasa rayukansu. Kodayake yan adawa sun sanar da cewar matasan da ke goyon bayan shugaba Mugabe sun yiwa wani dan jamiyyar aedawa ta MDC dukan da ya aika da shi lahira.

Duk da wanan an sami ci gaba domin yan adawa sun gudanar da yakin neman zabensu a bainar jama’a, ba kaman a lokutan baya ba da a boye suka gudanar da yakin neman zaben.

Ana sanya idanu sosai a zaben wakilan majalisar dokokin su 120 a kasar ta Zimbabwe, domin tanatance ko Mr Mugabe zai aiki da dokokin zaben da shugabanin yankin suka tsara bara.

Shugaban na Zimbabwe ya bullo da sabbin dokokin zabe domin kaucewa magudi, amma yan adawa sun hakake cewar lallai za’a tafka magudi a ranar zabe, kuma duk da cewar an yi yakin neman zaben cikin kwanciyar hankali, amma jamiyyar ZANU- PF ta yi amfani da barazana da turssasawa talakawa a yankunan karakara.

A yanzu shugaba Mugabe na fatan ganin cewar wakilan kasashen Afrika da zasu sanya idannu a zaben na gobe zasu amince da shi, domin ya sami saukin suka daga kasashen duniya, tare da baiwa zaben damar zama hallatace.

Shugaba Mugabe ya kosa ganin ya jawo kasashen duniya a jiki don su yarda cewar an sami ci gaban dimukrdiyya a kasar, idan aka kwatanta da zabbukan shekarun 2000 da na 2002 da ke cike da rigingimu ,magudi da murdiyar kuru’u.

Sai dai tuni kungiyar tarayyara Turai da Amurika sun yi kakausar suka a kann tsarin zaben suna cewar wasan yara ne, kuma an tsara shi ne domin kawai jamiyyar gwamnati ta sami nasara.

Amurika Ta bayyana damuwarta a kann nuna bambanci da ake yi a tsarin zaben na kasar Zimbabwe.

Uwaisu Abubakar Idris.