1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Najeriya shugaba Buhari ne kan gaba

Abdoulaye Mamane Amadou
February 26, 2019

A Najeriya a yayin da hukumar zaben kasar mai zaman kanta INEC ke ci gaba da bayyana sakamakon zabe, kawo yanzu Shugaba Muhammadu Buhari na APC na kan gaba a jerin 'yan takara.

https://p.dw.com/p/3E87u
Nigeria - Wahl verschoben
Hoto: Reuters/S. Maikatanga

A Najeriya har yanzu Shugaba Muhammadu Buhari shi ne ke kan gaba a kwarya-kwaryar sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ke cigaba da sanarwa.

Kawo yanzu Muhammadu Buhari mai shekaru 76 ya lashe zaben da jihohi 10) a yayin da abokin hamayyar sa Abubakar Atiku ya tashi da jihohi biyar 8.

Hukumar zaben ta sake komawa bakin aiki a yau Talata bayan ta dage zaman fadin sakamakon zaben  jihohi 12 daga cikin 36 na Najeriyar a daren jiya.

Ana bayar da sakamakon ne a daidai lokacin da jam'iyyar adawa ta PDP ta fitar da sanarwar zargin jam'iyyar APC da ke mulkin kasar da neman murda sakamakon zabe.