1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Mozambik

Abdourahamane HassaneOctober 14, 2014

Wannan zaben shi ne na biyar da kasar ta Mozambik za ta gudanar tun bayan lokacin da ta samu 'yancin kai a shekarun 1975

https://p.dw.com/p/1DVY8
Wahlkampf 2014 Mosambik Renamo Afonso Dlhakama
Hoto: picture-alliance/dpa

Ranar Laraba ake gudanar da zaben shugaban kasa a Mozambik da ma sauran zabukan 'yan majalisu. 'Yan takara guda uku ne zasu fafata a zaben shugaban kasar wanda ake da ji karar barkewar ringigimu bayan bayyana sakamakon.

Daga cikin 'yan takara ukun akwai Filipe Jacio Nyusi daya daga cikin 'yan gani kashenin shugaba mai barin gado wato Armando Guebuza wanda jam'iyyar da ke yin mulki ta Frelimo ta wakilta shi a matsayin dan takarata.

Filipe Jacio mai shekaru 55 da haifuwa shi ne ke riƙe da matsayin ministan tsaro na kasar wanda kuma bai taba rike matsayi ba a cikin kwamitin zartaswa na jam'iyyar ta Frelimo. Ya yi karantunsa a Jamhuriyar Chek da Ingila kafin a shekarun 1992 ya shugabancin kamfanin sufuri na jiragen kasa da na tashar jiragen ruwa na Mozambik. Ana dai yi masa kallon dan takara na tazarce, na ci gaba da aiwatar da manufofin Frelimo, bayan mulkin Geubuza.

Wahlkampf 2014 Mosambik Renamo Afonso Dlhakama
Madugun 'yan adawa Afonso Dlhakama na RenamoHoto: picture-alliance/dpa

'Yan takara daga jam'yyun Renamo da MDM

Akwai kuma Alfons Dhlakama jagoran tsohuwar kungiyar 'yan tawaye ta Renamo wacce ta kwashe kusan shekaru 20 ta na yaki da gwamnatin 'yan Frelimo. Dhlakama mai shekaru 61 da haifuwa yana rike da jaograncin jam'iyyar Renamo tun daga shekarun 1979. Ya gudanar da kamfe dinsa a karkashin tutar samar da kyakyawar rayuwa ga talakawa.

Dan takara na uku shi ne Daviz Simango mai shekaru 50 da haihuwa wanda aka kafa jam'iyyarsa ta MDM a shekarun 2009 ta sami rinjaye sosai a zaben kanana hukumomin da ta gabata.

Simango wanda ya yi zama a jamiyyar Frelimo tun lokacin samun 'yancin kai a shekarun 1975, ya fara siyasa ne a jam'iyyar 'yan adwa mafi girma ta Renamo kafin ya raba gari da ita ya kafa tasa jam'iyyar.

Wahlkampf 2014 Mosambik Filipe Nyusi
Filipe Nyusi wanda ake hasashen mai yiwuwa ya lashe zabeHoto: picture-alliance/dpa

Sabanin baya da ake zaton zai yi tasiri yanzu

A shekarun 2013 jam'iyyar Renamo ta kauracewa zaben kananan hukumomin da aka gudanar a kasar domin nuna bacin ranta akan abinda ta kira saba yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma tun a shekarun 1994 wacce ta kawo karshen yakin basasar kasar. Abin da ya sa Dhlakama ya sake komawa jeji tare da yin barazanar daukar makami amma a yanzu a sanssanta

Tuni dai jami'an da ke saka ido a zaben daga kasashen duniya suka isa kasar ta Mozanbik kuma masu lura da al'amura na hasahen cewar ba mamaki dan takarar jami'yyar da ke mulki ta Frelimo mista Filipe Jacio ya wuce tun zagaye na farko na zaben, idan ko har aka kai ga yin zagaye na biyu to kam akwai yiwuwar al'amura su canza kuma abubuwa na iya kara daburcewa kasar.