1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman ɗar-ɗar a Japan sakamakon mummunar yanayi

July 8, 2014

Jama'a na cikin fargaba a sakamakon sanarwar da hukumar binciken yanayi ta bayyana na zuwan wata guguwar mai ƙarfin gaske haɗe da iska da ruwan sama.

https://p.dw.com/p/1CXtI
Japan Taifun Neoguri 8.7.14
Hoto: Reuters

Hukumomi sun ba da umarnin kwashe mutane kusan dubu ɗari, waɗanda ke zaune a tsibirin Okinawa da zagaye, wanda ke a yankin kudu maso yammaci na ƙasar Japan. Saboda wata guguwa mai ƙarfin gaske da ke haɗe da iska da ruwan sama,kamar yadda jami'an bincike yanayi na ƙasar suka bayyana.

Guguwar wacce ke tafe da iska mai gudun kilomita 250 a awa, tare da toroƙon igiyar ruwar da ka iya kai mita 14 na iya janyo babban bala'i a ƙasar. Yanzu haka an soke tashi da saukar jiragen sama da na ruwa a tsibirin na Okinawa tare da rufe makarantu da kamfanoni a tsawon yini yau.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman