1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman dakarun Turai a Afirka ta Tsakiya

October 1, 2014

Tarayyar Turai za ta tsawaita zaman dakaru a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

https://p.dw.com/p/1DOWI
Hoto: Pacome Pabandji/AFP/Getty Images

Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana shirin tsawaita dakarun kiyaye zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da watanni uku, zuwa tsakiyar watan Maris na shekara mai zuwa.

A wannan Laraba kungiyar ta tabbatar da haka, domin karfafa zaman lafiya bayan watanni 18 da aka kwashe na rikici tsakanin bangarorin Saleka ta galibi Musulmai da kuma 'yan anti-Balaka. Ranar daya ga watan Afrilu Tarayyar Turai ta kaddamar da aikin dakaru 750 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, domin tallafa wa sojojin Faransa da na Tarayyar Afirka.

Kwamandan dakarun dan kasar Faransa ya nunar da mahimmancin tsawaita zaman dakarun, yayin da tuni Majalisar Dinkin Duniya ta karbi ragamar tafiyar da dakarun Afirka gami da kari daga wasu kasashe.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu