1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman lafiya tsakanin Kagame da Kabila

February 24, 2013

Kasashen da ke makobtaka da Kwango Demokaradiya sun yi alkawarin kawo karshen katsalandan da suke yi mata lokacin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/17ktz
Hoto: AP

Kasashe 11 na yankin tsakiya da kuma kudancin Afirka sun rattaba hannu akan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiyar Jamhuriyar Demokaradiyaa kwango. Daga cikin wadanda da suka yi tattaki i zuwa birnin Addis ababa domin shaidar da wannan biki, har da shugabanni Tanzaniya da na Rwanda da na Mozambik da na Afirka ta kudu da kuma takwaransu na Kwango Demokaradiya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon wanda ya yi ruwa da tsaki wajen ganin cewa a cimma wannan yarjejeniya, ya danganta ta da wani sabon babi da zai kawo karshen yakin basasa na shekaru 20 a Kwango. Wannan yarjejeniyar dai ta haramta wa kasashen da ke makobtaka da kwango yi mata katsalandan cikin harkokinta nacikin gida musamma dai na tsaron da ta ke fama da su. kana ta tanadi kawo karshen marawa 'yan tawayen kasashen Kwango da Rwanda baya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar