1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman rashin sanin tabbas a Kidal

July 22, 2013

Bayan barkewar rikici da sace jami'an zabe a Kidal na arewacin Mali, ana ci gaba da baiyana shakkar ko zai yiwu a gudanar da zabe a yankin daidai lokacin da aka shirya kada kuri'u na kasa baki daya

https://p.dw.com/p/19C0o
Hoto: Reuters

Ana iya cewa, kura ta dan lafa a yakin Kidal dake arewacin kasar Mali, bayan rikicin da ya barke tsakanin kabilar Abzinawa da bakar fatar dake zaune a yankin na Kidal a cikin makon da ya gabata, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu sa'annan da dama su ka ji rauni tare kuma da kona kasuwar yankin.

Wannan rikici da kuma awon gaba da aka yiwa wasu jam'in hukamar zabe guda biyar da daya daga zababbun yankin na Kidal, wadanda daga bisani aka sallamesu, sannan da wani bom da aka gano a yankin, ya soma kawo shakkar ko za a samu gudanar da zaben shugaban kasar na ranar 28 ga watan Yuli a yankin na Kidal. Wata matsala kuma da ake fuskanta a game da shirye-shiryen zaben shugaban kasar ita ce ta akwai katunan zabe kusan dubu 700 da ba su samu shiga ba a kan lokaci.

To sai dai duk da wadannan matsalolin a yanzu haka 'yan takara daban-daban na ci gaba da ba da mahimanci ga wannan zabe, inda a makon da ya gabata ma wasu kungiyoyin addinin Islama suka gudanar da wani taro wanda a karshensa su ka fitar dan takararsu mai suna Ibrahim Bubakar Keita, a karkashin jami'iyar da ake kira Sabati. Musa Boubakar Bah shi ne shugaban jam'iyar.

Mali - Interimspräsident Dioncounda Traore
Shugaban rikon-kwarya na MaliDioncounda Traore(dama)da shugaban Abzinawan AZAWAD Ibrahim Ag Assaleh.Hoto: Getty Images

"Ya ce mun gano cewa, lokaci ya yi da 'yan uwa Musumi za su yi ruwa da tsaki a game da lamarin siyasar kasar saboda da akwai babban kalubale a gabanmu. Matsalar kasar Mali a yanzu ta kasance matsala ce ta kasahen duniya, kenan magance wannan matsala zai fito ne daga kasashen duniya."

Kashi 80 a cikin dari na al'ummar kasar Mali Musulmi ne, hakan kuma ya kasance wani babban makamin yakin neman zabe ga wasu 'yan takarar, to sai dai a nasa bangaren Iman Mahamadu Dillo, shugaban wata kungiyar addinin Islama ya yi tsokaci a game da hanyoyin da 'yan takara suke bi wajen gudanar da yakin neman zabensu.

"Ya ce, sun mayar da Masallatanmu guraren yakin neman zabe, muna adawa da haka, mu a ganinmu kowa ya je a sassan kasa ya yi yakin neman zabe, Masu addini su gudanar da addininsu, 'yan siyasa kuma su yi siyasarsu, idan masu addini suka shiga siyasa to ba mu san inda za a je ba."

Mali Wahlvorbereitung für die Präsidentschaftswahlen
Shirye-shiryen zaben shugaban kasa a MaliHoto: DW/K.Gänsler

A game da halin da kasar ta Mali ke ciki a jajibirin zaben, shugaban gwamantin rikon kwarya Dioncounda Traore ya gana da wata tawaga ta 'yan tawayen MNLA da kuma ta AZAWD wadanda suka tattauna akan maganar kwanciyar hankalin kasar ta Mali, inda ma a ranar Litinin aka gudanar da wata sabuwar tattaunawar wacce ta maida hankali a kan yarjejeniyar Wagadugu ta 18 ga watan Yuni.

Mawallafi: Yusuf Abdoulaye
Edita: Umaru Aliyu