1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kubutar da mutane 100 daga hannun 'yan bindiga

Abdoulaye Mamane Amadou
July 21, 2021

Hukumomi a Jihar Zamfara sun tabbatar da kubtar mutun 100 galibi mata da yara kwanaki 42 bayan da 'yan fashin daji suka yi garkuwa da su a Kauyen Manawa.

https://p.dw.com/p/3xlXT
Nigeria Freilassung entführter Schülerinnen
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Rundunar 'yan sandan Jihar Zamfara da ta tabbatar da sakin mutanen, bata yi wani karin haske kan batun biyan kudin fansa ga maharan ba a ganin sakin.

Tun a farkon watan Yunin da yagaba ne dai wasu maharan dauke da muggan makamai suka yi awon gaba da mutanen, bayan sun yi dirar mikiya a kauyen Manawa da ke jihar ta Zamfara a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, yanakin da ya yi kaurin suna wajen yin garkuwa da jama'a don neman kudin fansa a Najeriya.