1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Brazil ta janyo asarar rayuka

April 20, 2014

Masu zanga-zanga a Brazil sun cinna wa motoci wuta bayan 'yan sanda sun kashe wasu matasa biyu.

https://p.dw.com/p/1BlLE
Hoto: Reuters

Mazauna birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil da suka harzuka sun cinna wa motocin safa-safa wuta, domin nuna rashin jin dadi da kisan wasu matasa biyu da 'yan sanda suka yi, lokacin wata hatsaniya.

Masu zanga-zangar kimanin 30 sun toshe wata unguwa da ke birnin, abin da ya kawo cikas wa masu tafiya gudanar da bukukuwan Easter da mabiya addinin Kirista ke yi ko'ina a duniya. Mahukuntan kasar ta Brazil na ci gaba da daukan matakan karfafa harkokin tsaro yayin da rage kimanin watanni biyu a fara wasan neman cin kofin kwallon kafa na duniya da kasar za ta dauki nauyin shiryawa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal