1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Sao Paulo

Nicole ScherschunJune 9, 2014

'Yan sanda kwantar da tarzoma a birnin Sauo Paulo na Brazil sun yi amfani da kulake da barkonon tsofuwa domin tarwatsa wasu ɗaruruwan matasan da ke yin zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/1CEy9
Sao Paolo Streik Ausschreitungen 9.6.2014
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Masu aiko da rahotannin sun ce mtasan sun datse hanyoyi da shingaye a tsakiyar birnin inda suka cina wuta ga kondaye na shara da kuma tayoyi, tare da kawo cikas ga al'amuran zirga- zirga. Yayin da ya rage kwanaki uku a soma gudanar da gasar cin kofin duniya na ƙwalon ƙafa a Brazil.

Har yazuwa yanzu an gaza cimma daidaito tsakanin gwamnatin da ƙungiyoyin ƙwadago na sufurin jiragen ƙasa da motocin bus da ke yin yajin aiki a Saulo Paulo inda nan ne za a buɗe wasannin ran Alhamis mai zuwa.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman