1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga na kara kamari a Italiya

December 12, 2014

Hadaddiyar kungiyar kwadagon kasar Italiya ta sha alwashin ci gaba da yin zanga-zangar nuna kin amincewa da sabuwar dokar tsuke bakin aljihu da mahukuntan kasar suka fito da ita.

https://p.dw.com/p/1E3Ug
Hoto: AFP/Getty Images/G. Bouys

Dokar dai ta amince da yi wa dokokin aiki a ma'aikatu da hukumomin gwamnatin kasar ta Italiya kwaskwarima, wanda kuma ka iya kaiwa ga korar ma'aikata masu yawa. Firaministan kasar ta Italiya Matteo Renzi ne dai ya gabatar da wanna doka, inda kuma hakan ya sanya dubun-dubatar 'yan kawadagon Italiyan fitowa kan tituna suna masu zanga-zangar nuna adawa da wannan doka. Wannan gagarumar zanga-zanga dai na zaman kalubale na farko da gwamnatin Firaminista Renzi ta fuskanta tun bayan da ya dare kan karagar mulki a watan Fabarairun da ya gabata.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman