1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu na fuskantar zanga-zanga

Lateefa Mustapha Ja'afarOctober 14, 2015

Dubban masu zanga-zanga a Afirka ta Kudu sun bazu a titunan birnin Johannesburg domin nuna adawarsu da almundahana da kudaden jama'a da suke zargin gwamnatin kasar da yi.

https://p.dw.com/p/1GoSz
Zanga-zangar adawa da cin hanci a Afirka ta Kudu
Zanga-zangar adawa da cin hanci a Afirka ta KuduHoto: picture-alliance/dpa/K. Ludbrook

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin kasar ke ci gaba da fuskantar fushin al'umma sakamakon halin tabarbarewar tattalin arziki da kasar ke kara shiga. Kungiyar ma'aikatan sarrafa karafa ta kasar "NUMSA" da ke zaman babbar jagorar adawa da jam'iyyar Shugaba Jacob Zuma ta ANC a Afirka ta Kudu ce ke jagorantar zanga-zangar. Masu zanga-zangar dai na dauke da tutoci da ke dauke da rubutu kamar haka: "A yi waje da gwamnatin Zuma" da kuma wani rubutun da ke cewa: "Masu almundahana na karbar haraji daga wajen talakawa".